CIKAKKEN BAYANI, DALILIN DA YASA AKA HANA 'YAN SHI'A YIN TATTAKIN ASHURA


Kamar Yadda BBC HAUSA ta rawaito. Rundunar 'yan sanda a Najeriya ta ce ba dukkan Musulmai ta
haramta wa yin tattakin Ranar Ashura ba, sai 'ya'yan kungiyar
Islamic Movement of Nigeria (IMN) wato mabiya bayan
Sheikh Ibrahim El-Zakzaky.


"Biyo bayan neman karin bayani da mutane ke yi kan haramta
kungiyar IMN, ya zama wajibi a sani cewa haramcin yin
tattakin ya shafi 'ya'yan kungiyar IMN din ne kawai.
"Saboda haka sauran al'ummar Musulmi da suke da sha'awar
yin tattakin Ashura a fadin Najeriya za su iya bin sahun sauran
Musulmin duniya domin yin haka."


Following the deluge of enquiries concerning the ban on
procession on the proscribed Islamic Movement in
Nigeria (IMN), it has become absolutely imperative to
clarify that the ban on processions is applicable to
members of the proscribed Islamic Movement in
Nigeria only.
— Nigeria Police Force (@PoliceNG) 10 Satumba, 2019


Against this backdrop, Muslims marking the
commemoration of “Ashura” throughout the country
along with other Muslims across the world are free to
carry out the annual “Ashura” procession.
— Nigeria Police Force (@PoliceNG) 10 Satumba, 2019

Amma duk da wannan haramci tuni 'ya'yan kungiyar ta IMN
suka fita yin tattakin a jihohi da dama na Najeriyar.
Kuma tuni kungiyar ta ce jami'an tsaro sun kashe mata mutum
uku a Kaduna da Gombe da Katsina da Ilela ta jihar Sakkwato
da kuma Bauchi a tattakin da suka fita yi na Ranar Ashura.


Sai dai rundunar 'yan sandan jihar Kaduna ta tabbatar wa da
BBC cewa ba su harbi ko da kiyashi ba, amma sun fatattaki
'yan shi'ar mabiya IMN a lokacin da suka fito tattakin.
Kungiyar ta IMN ta wallafa wasu hotuna a shafinta na Twitter
mai suna @SZakzakyOffice, inda ta ce su ne na mutanen da
jami'an tsaron suka harbe mata.


Ta kara da cewa an yi tattakin lafiya an watse a jihar kano ba
tare da hargitsi ba kamar sauran sassa.

Ashura mourning procession earlier today in Kano, the
procession ended peacefully, as it's not attacked by
Nigerian securities like in other places. pic twitter.com/ PDF6wxw9KD
— Islamic movement in Nigeria (@imnigeria_org) 10
Satumba, 2019


Tun da fari Kungiyar IMN ta bakin kakakinta Ibrahim Musa ta
lashi takobin yin jerin-gwanon a jihohin kasar duk kuwa da
gargadin da rundunar 'yan sanda ta Najeriyar ta yi na jaddada
haramcin duk wasu ayyuka nata.
Ranar Talata ce 10 ga watan Muharram da 'yan shi'a suke yin
tattakin Ranar Ashura da aka kashe jikan Manzon Allah SAW,
Imam Hussaini dan Aliyu dan Abi Talib.
Mabiya Shi'a a duniya na gudanar da jerin gwanon domin nuna
bakin cikinsu da kisan na Imam Hussaini ibn Ali, a yakin

Karbala.

No comments:

Join our WhatsApp group

Join our WhatsApp group
Latsa nan domin shiga group din mu na whatsapp
Powered by Blogger.