MALAMIN ADDINI YA MUTU SAKAMAKON YUNKURIN YIN AZUMIN KWANA 40 IRIN NA ANNABI ISAH

MALAMIN ADDINI YA MUTU SAKAMAKON YUNKURIN YIN AZUMIN KWANA 40 IRIN NA ANNABI ISAH
Wani fasto a Afirka ta Kudu, mai suna Alfred Ndlovu ya mutu saboda rashin abinci mai gina jiki bayan an kwashe tsawon kwanaki 30
 a lokacin da ya yi kokarin ya kwaikwayi Yesu wato Annabi Isah da yayi azumi Kwana 40 da dare arba'in.

 Kamfanin Buzz na Afirka ta Kudu ya ba da rahoton cewa, Faston mai shekaru 44
  ya bar gidane a ranar 17 ga watan Yuni zuwa wani daji dake kusa da shi inda yake yin addu'o'i, kamar yadda Yesu ya yi.  Sai dai kuma faston mai suna Alfred Ndlovu a kokarin shi na kwaikwayon Yesu domin yin azumin Kwanaki 40, Mista Alfred Ndlovu ya mutu wata daya kacal

Duk da kasancewa ba'a san dalilin rashin lafiyar tasa ba domin Shi kaÉ—ai ne a cikin jeji kuma an samu bayanin ganin gawarsa ne a bakin baÆ™o wanda ya kira 'yan sanda. 


Labarin mutuwar faston ta girgiza iyalansa da wasu manyan malaman cocinsu har ma da membobin cocin.


Wani makusancinsa ya ce: Faston 'Ya kasance mutum mai son jama'a ne. Munyi takaici da jin ya mutu ta wannan hanyar.  Bayan
 wata daya muka sami labarin bakin ciki game da rasuwarsa. Yaci gaba da cewa
 Fasto É—an dattijo ne mai lafiya da addini wanda
 bai ma duba shekarun sa ba.

Domin neman karin bayani Latsa nan

No comments:

Join our WhatsApp group

Join our WhatsApp group
Latsa nan domin shiga group din mu na whatsapp
Powered by Blogger.