WATA SABUWA: AN BANKADO ASIRIN BOYE ASHE TUN FARKO AN ZALUNCI AISHA BA KADAN BA KAFIN TAYI YUNKURIN KASHE KANTA


KAFIN KU LA'ANCI AISHA DA TA BANKA MA KANTA WUTA ZAN SO KU JI WANNAN LABARIN MAI DAUKE DA TAUSAYI.

Kamar yadda Jaridar Jakadiyar Zamfara ta wallafa a shafinta na Facebook Ashe tun farko anzalunci Aisha bakadan ba, kafin har ta yanke hukuncin kashekanta, Aisha tana tare da saurayinta mai matukar sonta sun shaku da juna matuka wuce misaltuwa, bayan samun wannan shakuwa sai uwayenta suka yanke hukuncin cewa ba za ta auri wannan saurayi ba, aka gabatar mata wanda akeso a aura mata, Aisha ta kafe kai ga kasa cewa ita bata son wannan da iyayenta suke so, a sanadin haka lokaci zuwa lokaci Ana gana mata azaba duka da zagi hadi da tsan gwama.


Tana cikin wannan hali na azabtarwa sai matar babanta mai suna luba ta koreta a gidan, bayan luba ta koreta a gidan ba ta zame ko inaba sai gidan yayarta (Antynta) bayan ta tare a gidan yayarta sai wannan saurayin nata da suke tsananin kaunar juna ya biyota a gidan antynta, yana zuwa fira lokaci bayan lokaci, da iyayenta suka fahimci cewar wannan saurayin yana nan yana zuwa a can gidan yayarta sai suka bita a gidan suka makamata mugun duka na fitar hankali, sai suka dawo da ita a gida aka sakata a cikin daki, suka sa garwashi (garwasu) tare da barkono ( Taush-shi) a cikin wannan garwasu, aka kulleta acikin dakin tasha buraren bala'in barkono, bayan ta sha wannan azaba taki aminta da wanda iyayenta suke ra'ayi.


Tsugunne bata kareba sai aka sake daka barkono (Taush-shi) aka saka mata a cikin al'aura Wa iya zubillah, Aisha tasha azaba tayi buge buge kamar zata mutu, bayan wannan mummunan hukunci da ta sha, da ga bisani sai ta yanke shawarar aikata abunda ta aikata, domin binne abubuwanda za ta iya fuskanta matakin gaba.


Ya Salam Aisha tabbas ta yi kuskure na yunkurin kashe kanta da kanta, amma mai karatu abunda ya kamata mu fahimta anan wannan ba yunkurin kashe kai bane, yunkurin kisan kaine. A halin yanzu dai Aisha na Asibiti karkashin kulawar likitoci Allah ya bata lafiya Ameen

No comments:

Join our WhatsApp group

Join our WhatsApp group
Latsa nan domin shiga group din mu na whatsapp
Powered by Blogger.