DABARU GOMA SHA DAYA DA ZAKI ZAUNA DA UWAR MIJINKI LAFIYA

DABARU GOMA SHA DAYA DA ZAKI ZAUNA DA UWAR MIJINKI LAFIYA





Uwar mijinki ta na da mutuqar mutunci da daraja, domin mijin da ki ke taqama da shi danta ne, ita ta dauki cikin shi wata tara, ta haife shi, ta raine shi, ta yi wahala da shi, har ya girma kika aure shi da hakoransa cif a baki, kafin ya aureki uwar shi ya sani da 'yan'uwan sa, yanzu kuma ga ki kin shigo Family din su, sai kice uwar shi itace abokiyar gaban ki? Wannan babban kuskure ne. Yanzu 'yan mata har sunaye suke sama iyayen mazajensu, wai uwar miji musifa ce, uwar miji bala'I ce, uwar miji hawan jini ce, waiyazu billah, wacce ta haifi uban 'ya'yan ki itace musifa, lallai kuwa kin dauko hanyan rusa auren ki. Dole ne ki mutunta ta, dole ne ki so ta, kuma ko kin 'ki, ko kin so matsayin uwa take a wurin ki. Ya ke 'Yar'uwata! Mai shirin shiga dakin mijinta ki sani, uwar miji mutumiyar kirki ce, uwar miji masoyiyar ki ce, uwar miji tana da mutunci a idon ki, idan kin dauke ta a haka to ga wasu dabaru nan da za ki yi amfani da su wurin mallakar uwar mijin ki ba BOKA BA MALAM. . "RAYUWAR 'YAN AREWA" 1. Mutunta ta, Idan za ki gaishe ta ki gaishe ta da mutuntawa, idan zaki yi mata magana kiyi mata magana da mutuntawa. . 2. Kyautata mata, Ki yi kokari wurin kyautata mata, kyauta ne, yi mata dinki, yi mata girki, idan tana buqatar wani abu ki siya ki bata, idan abinci ne abinda ta fi so shi za ki rinqa bata, idan ma ba unguwar ku daya ba, sai ki rinqa yi ana aika mata da shi lokaci zuwa lokaci. . 3. Idan ki na son ki sami karbuwa to fa ki kula da irin maganganun da za ki rinqa furtawa a gabanta, ka da ki sa ke ki yi maganar da ba zata so ba, idan ma kin yi ne kika ga bata so ba to sai ki nemi afuwarta. . 4. Ki rinqa ambata ma uwarsa abin da danta ya ke yi na alkhairi, misali idan yana tallafawa wata makaranta, ko taimakama wasu gajiyayyu, kada ki rinqa ambata mata yana siya miki kaza da kaza domin wata uwar mijin sai hassada ta kamata ta tada hankalinta, tace kin mallake shi, ai sai abin da kika ce ya ke yi, shikenan sai ta tsaneki. . 5. Ki rinqa kwadaitar da mijin ki akan ya rinqa ziyartar su, ko da kuwa a gari 'daya suke. . 6. Sannan ki rinqa kwadaitar da shi daukan ki da 'ya'yanki ku je ku wuni mata, kin ga zata ji dadi, kuma ki kwabi 'ya'yanki kafin kuje, domin kada su yi ta mata dambe da rashin kunya da 'barna, su sa taji haushin ki tace baki ba ma jikokinta tarbiyya ba. . 7. Sannan duk qawayen uwar mijinki ki rinqa girmama su suma, kuma ki rinqa musu kyauta daga lokaci zuwa lokaci, hikiman yin haka shinen duk abin da ki ka ba su za su bata labari, kin ga zata ji dadi ta qara sonki. . 8. Idan mijinki zai siyawa mahaifiyarsa zani, to kada ki yi mugunta, ke ki sa Super ita kice a siya mata 'yar dubu biyu, wanda ba zai kai ko ina ba zai kode, idan ya siya miki mai kyau itama ki ce ya siya mata mai kyau. . 9. Ki rinqa tunatar da shi wurin siya musu kayan abinci,da yi musu sutura akai-akai, domin da ban tausayi ka ga namiji gidansa ana cin kaji amma miyan mahaifiyarsa kamar ruwan wanke kai, wallahi sai Allah ya saka. mata, idan ya siyo kaji goma ko bai ce ba, ki ce wane zan cire biyu inyiwa Inna miya muje a kai mata, kuma shi ma zai qara sonki. . 10. Sannan ko da wasa ka da ki sa ke ki rinqa zagin uwar mijinki, domin wallahi magana fa yana zagayawa, za ki yi mamakin jin maganganun banzan ki ya kai kunninta, babu ruwan ki, ko da ki na kyautata mata amma bata sonki ki cigaba wata rana zata soke, idan har kina kyautata mata. . 11. Sannan idan kinje yi mata wuni, to fa kada ki zauna baki komai, daki yayi datti ki 'ki gyarawa ki share, inmaso samu ne kina zuwa ki fara mata hidima, ki kwaso kayanta ki wanke, ki share ciki da wajen dakin, ki mata gogye gogye, wata ma idan ta iya kitso har tsefe kan uwar mijinta take yi, ta wanke mata ta rangada mata kitso, ko kuma tace a kira mai kitso ta biya kudin ayi mata. . Wainnan duka muna daukan su abin wasa, amma ba haka bane, rashin kula da su yasa iyayen mazajen mu suke takura mana, suke tsanar mu, kuma wani lokacin suna da gaskiya, domin tunda kika auri dansu gaishe su ma ya daina zuwa, ke kuma bakya kwadaitar da shi, duk inda kika zauna ki zagye ta, idan za ai mata zani mai tsada ki hana, baki zuwa gaishe ta, kinje mata wuni kina cika kina batsewa, dole ta tsaneki, tace asiri kike masa koda kuwa ba haka bane, suma 'yan'uwansa dole su tsane ki domin mahaifiyarsa bata sonki.

No comments:

Join our WhatsApp group

Join our WhatsApp group
Latsa nan domin shiga group din mu na whatsapp
Powered by Blogger.