SAMUN SOYAYYAR GASKIYA SHINE BURIN KO WANE MASOYI

BURIN KO WANE MASOYI SHINE SAMUN MASOYI NA GASKIYA, 

Da za ace a bayyana kunci da zuciya ke shiga a
sanadin soyayya Dana tabbata abubuwa sun
chanza.


 Amma masoya karku yanke kauna daga rahamar
ubangiji,
nasan soyayya alkairine


 kar kuyi kokarin
bakantawa
zuciyar da tarin sirrika suke boye a cikinta, masoya
kada
kuyi sanadiyar zubar hawaye daga idanuwan da
tarin
al'umma suke samun walwala dominsu


Cutuka iri-iri ne amma bana tunanin akwai mai
dafi kamar cutar so.


 Soyayyar gaskiya tamkar
fatalwace
wacce kowa zai fada amma kalilan ne suka ganta

soyayya ta gaskiya bata rabuwa da farin ciki har
abada kuma sannan bata da karshe. Masoya Ku
sanyawa zuciyarku aminci da soyayya kawai kuci
gaba
da tafiya a tsarin so.


Abinda na fahimta kawai soyayya tsakanin namiji
da
mace tilas ne idan ba haka ba kuwa mutuwa ta
wajaba ga dayansu duk ranar da masoyi yayi
bankwana da dayansa ina da tabbacin walwala
tayi bankwana da wannan masoyin ba.


Abun
da ciwo
kaso mutum ba tare da Wanda kake so yasan
kanayi ba,
amma kuma bana tunanin akwai abinda yafi ciwo
fiye
da kaso mutum amma ka kasa samun kwarin
guiwar
ka furtawa Wanda kake so cewa kana sonsa.


Ubangiji yana jarabtarmu da soyayya ta karya
mai
cike da tarin rudani daga bisani kuma ya nufemu
da
samun soyayya ta gaskiya saboda mu fahimci
wacce
irin ni'ima yayi mana a gaba.


soyayya tana
kamuwa da
zuciyar da namiji ta cikin kwayar idanuwansa ne
ita kuma "ya mace tana kamuwane ta cikin
kunnuwanta
a lokacin da alaka ta tayi nisa a tsakanin da
namiji da
'ya Mace ta yuyu mutuncine a tsakaninka da
ita
idan ya kasance a cikin alakar da akwai tausayi
da
kyautatawa juna soyayya na iya samun
matsuguni a
cikin zuciyar kowanensu.


Yana daukar ka minti kachal kaji kana ra'ayin
mutum
zai kuma iya daukarka kwana daya kaji ka kamu
da
son mutum amma zai iya daukarka har tsawon
rayuwa kafin ka manta da mutumin da ka kamu
da cutar son sa.


 Ako da yaushe bani da wani buri
face
naga kan masoya ya hadu a lokacin ne jindadi da wal-wala ke cika zuciyata


A karshe ina mai muku tuni da cewa jinkiri ga
yafiya
yakan zama Dana Sani, domin idan tsautsayi ya
kasance baya wuce ranarsa.


Toh ya za a kira
kaddara
da kowane dan Adam yana tare da irin nasa?.


Idan
tafiya tayi nisa waiwaye bai cika zama ado a
cikinta ba domin ita fa zuciya an halicceta ne tare da
soyayyar mai kyatata mata sannan babu abunda
ta
tsana sama da mai bata damuwa a cikinta



Ku kasance tare da MAMAKI TV DUNIYAR MASOYA

No comments:

Join our WhatsApp group

Join our WhatsApp group
Latsa nan domin shiga group din mu na whatsapp
Powered by Blogger.