YARINYA 'YAR PRIMARY TA KASHE KANTA SABODA MALAMINSU YA KYARE TA A LOKACIN DA JINI YA ZO MATA


Kamar yadda shafin watsa labarai mai zaman kansa na BBC ya rawaito. 'Yan sanda a kasar Kenya na gudanar da bincike kan dalilin da ya sa wata yarinya 'yar shekara 14 ta kashe kanta bayan da jinin al'ada ya bata mata kayan makaranta.

Mahaifiyar marigayiyar, Beatrice Chepkurui Koech ta ce malamin yarinyar ne ya kunyata 'yarta sakamakon jinin al'adar da ya lalata mata kayan makarantarta.
Mahaifiyar ta bayyana cewa, ''Ba ta da kunzugun da za ta sa, lokacin da jinin ya shafi kayanta, malamin ya kyare ta kan ta fice ta tsaya a wajen ajin.''

Wannan dalili ya sa mahaifiyar yarinyar tare da wasu iyayen yara kusan 200 suka gudanar da zanga-zanga a wajen makarantar firamaren da ke Kabiangek, wadda ke da nisan taku 270 daga yammacin babban birnin kasar, Nairobi inda suke neman a kama malamin da ake zargi da kyarar yarinyar.

A cewar jarida mai zaman kanta a Kenya ta Daily Nation, 'yan sanda sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye wajen tarwatsa masu zanga-zangar da su ka rufe titi abin da ya sa aka garkame makarantar


Babban jami'in 'yan sanda na yankin Rift Valley, Alex Shikondi ya ce ana gudanar da bincike kan al'amarin inda ya yi kira ga iyayen yara da su zama masu kusantar 'ya'yansu domin sanin halin da su ke ciki a koda yaushe.

Bisa dokar da Kenya ta amince da ita cikin Yunin 2017, gwamnatin kasar ce za ta rika samar wa 'yan mata na makarantun firamare audugar al'ada kyauta.


Wannan danyen aiki da matashiyar ta yi, ya sanya kwamitin majalisar dokokin kasar Kenya fara bincike kan dalilin da ya sa har yanzu shirin samar wa mata audugar al'ada, da gwamnati za ta rika kashe kimanin dala miliyan hudu da dubu 500 a shekara wajen samar da shi, bai fara aiki ba.

No comments:

Join our WhatsApp group

Join our WhatsApp group
Latsa nan domin shiga group din mu na whatsapp
Powered by Blogger.