ALAMOMI 16 DAKE NUNA ALAMUN MACE TA KAMU DA SON NAMIJI


ALAMOMI 16 DAKE NUNA ALAMUN MACE TA KAMU DA SON NAMIJI

1. KALLO: Mata suna aika sakonni da yawa ta hanyar kallo,
kamar So, raini, tsoro, ba ruwana dakai da sauransu, kuma
kowane ba sai an fassarawa mutum ba da ya gani yasan me
ake nufi


2. KULAWA: Wannan na nufin ta nuna ta damu dashi a
kowanne lokaci, ta hanyar kokarin jin halin da yake, lafiyarsa
da kuma al'amuransa. Ko yana kusa da ita ko kuma nesa da
ita. Idan abun murna ya sameshi ta tayashi idan na jaje ya
sameshi ta jajanta masa. Ba shakka wannan yana nuna
soyayya.


3. BIYAYYA: Mace ta rinka girmama namiji, abokansa da
'yan'uwansa a duk lokacin da zata mu'amalance shi ko su, a
gaisuwa ne, a magana ce, a rubutaccen sako ne duk
wadannan yana bukatar yaga ladabi acikinsu kada ta rinka yi
masa tsiwa da rashin kunya da sauran dabi'u da zasu nunawa
mutum ba a dauke shi abakin komai ba hakika wannan ma so ne.


4. HAKURI: Babban abinda yafi bada wahala a mu'amala
kuma a kafi jarraba mutum akai shine hakuri, ya zamanto
namiji ya gamsu da hakurin mace ta kowace hanya kar ta
rinka yi masa koke-koke, ko ta zama mai rainuwa, duk abinda
ya bata tayi hakuri dashi kar tace bai kai kaza ba ko kuma bai
kai na wance ba, idan sabani ya shiga kada tayi jayayya dashi
idan kuma taga yayi fushi ta rarrasheshi tace yayi hakuri.


5. UZURI: Anan ana nufin mace ta zama mai karbar
hanzarinsa duk lokacin da wani abu ya faru, misali, ta buga
masa waya bai dauka ba ko ta tura masa sako bai bata amsa
ba, kada tayi fushi tace shikenan tunda abin wulakancine
bazan sake kira ba, ta daure ta cigaba da neman jin me yake
faruwa kafin ta yanke hukunci, domin akwai dalilai da yawa
dake iya sa hakan ta kasance kamar rashin lafiya, faduwar
wayar da sauransu. Idan kuma ya kirata daga baya shima ta
dauka cikin farin ciki ba da fushi ba, har taji dalilinsa, kuma
koda ya kawo mata hujja ta karya kuma ta gane to tayi dariya
acikin ranta kawai kada ta nuna masa ta harbo jirginsa.


6. TAUSAYI: Mace ta zama mai tausayawa namiji don shi
namiji har kirari ake masa da cewa "Zakara mai neman suna,
bada kwaya kaci tsakuwa" saboda haka ta kalli wane shi da
idan basira kamin ta koro masa wasu bukatun, kada tasa ya
rinka jin tsoron zuwa gurinta, ko kuma da yaga kiranta
gabansa ya fadi don yasan matsala za'a karanta masa. Wani
kuma ba dora masa bukatar za a yi ba a'a, shi zai dorawa
kansa amma zai kokarin yin abinda yafi karfinsa don kar ace
ya gaza ko kuma ace kai wane BA dama! Da sauran dalilai, to
shi wannan birki za tai ta taka masa.


7. TATTALI: Duk abinda namiji ya yiwa mace tayi kokarin
tattala wannan abun, kada ta zama mai barna ko
almubazziranci don gadarar ko yanzu nace ya sake yimin
zaiyi.


8. SHAWARA: Idan namiji yaga a mafi yawancin lokaci mace
takan shawarceshi acikin wasu lamuranta na rayuwa wanda
shi yasan ba lallai bane ta sanar dashi kuma yasan ba wani
abinsa take jira ko sa rai ba kuma bashi kadai ya iya bada
shawaraba, to wannan yana bashi sakon cewa ana tare dashi.


9. ALFAHARI: Wato mace ta nunawa namiji shi wani ne a
gurinta, a gaban kowa, ko an tambayeta ko ba a tambayeta
ba, ba idan anji tana waya dashi a tambayeta wane tace 'wani
ne yake ta damuna nace ya daina kirana amma yaki' ko kuma
tace 'saurayin kawatane' muke gaisawa. A'a zakaji tace ni da (Ahmed) ta fadi sunanka muke gaisawa wannan ma alamar  so ne


10. KYAUTATA ZATO: Mace ta yiwa namiji zato na alkhairi
kada ta munana masa zato ko tai ta kokarin gano wadansu
kura-kurensa koda kuwa yanayi, matukar ya sirrintasu har sai
idan yaqini ya zo mata.


11. YAFIYA: Babu yadda za'ayi a gina mu'amalar da sabani
bazai shigo ba, don haka mace ta zama me afuwa ga namiji a
duk lokacin da sabani ya yazo, kada ta dage akan lallai ita
tana da hakki, koda tana dashi din ta yafe wannan zai kara
mata daraja ko ba a sannan ba ko zuwa gabane, kuma kada a
yafe a baki amma a zuciya.... Ko kuma ranar da wani sabanin
yazo ace dama rannan ma ... Kada tayi haka.


12. KYAUTATAWA: Ya zamana duk lokacin da zaije wajenta to
ta kyautata masa kada yaji cewa bata mutuntashi ba.


13. KARIYA: Shine mace ta zama me kare namiji daga
dukkanin abinda zai cutar dashi ko kuma mutuncinsa, ya
zamana wani ko wata bazai ci zarafinsa ba matukar tana
wurin koda kuwa danuwantane.


14. TSAFTA: Ya zamana duk lokacin da namiji zai hadu da
mace to ya ganta kamar sannan za'a kaita gidan miji .......


15. NUTSUWA: Mace ta zama mai sa namiji farin ciki a koda
yaushe, har ya zamto koda an bata masa rai a wani gurin ko
kuma wasu alamuran sun sha masa kai zai iya zuwa gurinta
ko kuma kiranta suyi maganar don yasan zata rarrasheshi har
ya sami nutsuwa da kwanciyar hankali.


16. GASKIYA: mace ta kasance mai bayyanar da gaskiyarta
ga namiji a duk abinda za suyi, kada karya, cutarwa, rashin
gaskiya ya fito a gurinta komai kankantarsa


Muna maraba da comments din ku, na wasu daga alamomin
da ba mu fada ba. Ku biyo mu a post din mu da ke nan tafe.

No comments:

Join our WhatsApp group

Join our WhatsApp group
Latsa nan domin shiga group din mu na whatsapp
Powered by Blogger.