BUDURWA TA CINNAWA KANTA WUTA SABODA IYAYENTA SUN RABATA DA SAURAYIN DA TAKE SO A ZAMFARA




BUDURWA TA CINNAWA KANTA WUTA SABODA IYAYENTA SUN RABATA DA SAURAYIN DA TAKE SO A ZAMFARA

 Kamar yadda BBC hausa ta wallafa wata matashiya mai suna Aisha Aminu wacce suke zaune a
Albarkaraawa a jihar Zamfara ta cinna wa kanta wuta saboda
an hana ta auren saurayin da take kauna.
Aisha ta shaida wa BBC cewa ta dauki wannan mataki ne
saboda ba za ta iya hakura da shi ba kuma "da ta yi karuwanci
gara ta kashe kanta" kawai.


Mahaifin Aisha Aminu Muhammad Albarkarawa ya shaida wa
BBC cewa saurayi ne take so tsawon shekara daya amma
Allah bai sa yana da abin aurenta ba.

"Saboda haka ne muka dakatar da shi da zuwa wurinta tunda
ba shi da abin aurenta har sai Allah ya kawo mata wani.," in ji
Aminu Muhammad.


Ya kara da cewa: "Ashe ita kuma tana sonsa sosai. Shi ne ta
dauki wannan mataki ba tare da saninnmu ba, kawai sai
ganinta muka yi tana ci da wuta, jama'a suka yti kokarin wutar.
"Da aka tambaye ta dalili sai ta ce ita wallahi tana sonsa ne
kuma da ta je ta yi iskanci gara ta kashe kanta tun da ba shi da
halin da zai iya aurenta."


Ita ma Aisha ta ce ta dauki wannan mataki ne saboda tana
sonsa kuma shi ma yana sonta.
Ta ce: "Na dauki wannan mataki ne saboda ina sonsa kuma
tun da muke tare da shi bai taba gaya mani wata magana ba.
"Acaba (okada) yake yi saboda haka sai ya yi zaton cewa ba
shi da wani hali. Ni kuma na ce da in je in yi karuwanci gara na
kashe kaina na huta kawai. Sai na sa ma kaina fetur kawai, na
sa ashana."


Aisha ta ce ta ji raunuka a hannayenta da bayanta da kuma
ciki, sannan kuma ta ce ta yi nadama.
Sai dai ta ce ba ta san halin da masoyin nata yake ciki ba a
halin yanzu domin har yanzu bai je dubiya ba.


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun labaran mu ta whatsapp

👇
https://chat.whatsapp.com/HgZWA4fKdCDCziNMbLrIXI

No comments:

Join our WhatsApp group

Join our WhatsApp group
Latsa nan domin shiga group din mu na whatsapp
Powered by Blogger.