ABUN KUNYA: BAYAN AN DADE ANA ZARGINSA DUBU TA CIKI AN KAMASHI KIRI-KIRI YANA LALATA DA AKUYA


ABUN KUNYA: BAYAN AN DADE ANA ZARGINSA DUBU TA CIKI AN KAMASHI KIRI-KIRI YANA LALATA DA AKUYA

An kama wani saurayi dan kasar Malawi mai suna Kennedy
Kambani mai shekara shekara ashirin da daya yana lalata da akuya, inda ya ce
sai da ya nemi izinin akuyar kafin ya yi lalata da ita.
Mai akuyar ya ce, ya yi zaton Kennedy Kambani zai sace
akuyar ce, sai ya gaya wa makwabta su rika kula da shi. Ya
ce bayan ya dawo gida ne makwabtansa suka ce sun kama
Kennedy Kambani yana yi wa akuyar fyade.


Sufeto Lubrino Kaitano ya ce, “Mai akuyar, Mista Pemphero
Mwakhulika ya yi tunanin Kambani zai saci akuyar ce, sai
shi kuwa ya sanar da jama’a abin da ke faruwa.”
Bayan da jama’a suka halarci harabar da aka kama
Kambani, sai suka razana ta yadda suka kama shi yana yi
wa akuyar fyade.


Bayan kama Kambani an mika shi ga ofishin ’yan sanda don
laifin yi wa dabba fyade. Sai dai a bangarensa, bai amsa
laifin fyade ba, saboda ya ce sai da ya nemi izinin akuyar
kafin ya fara lalata da ita.


Akuyar tana daya daga cikin wadanda suke kiwo a wajen
kauyen Mchinji da ke kasar Malawi.
Wani rahoto ya ce, a watan Nuwamban bara an kama wani
mai suna Reuben Mwaba mai shekara 22 yana yi wa
akuyarsa fyade a garin Kasama na kasar Zambiya.


Kuma a watan na Nuwamba an kama wani mai suna
Feselani Mcube mai shekara 33 yana yi wa akuyar
makwabcinsa fyade a gadonsa da ke unguwar Winterbeldt,
a kasar Afirka ta Kudu.

No comments:

Join our WhatsApp group

Join our WhatsApp group
Latsa nan domin shiga group din mu na whatsapp
Powered by Blogger.