YADDA WANI BERA YASA 'YAN MAJALISSA GUDUN FAN-FALAKI A FADAR SHUGABAN KASAR AMURKA

YADDA WANI BERA YASA 'YAN MAJALISSA GUDUN FAN-FALAKI A FADAR SHUGABAN KASAR AMURKA



A ranar Talatar nan da ta gabata ne 'yan jarida suka ga wani
abin mamaki, yayin da wani bera ya fado daga saman rufin
fadar shugaban kasar Amurka wato 'White House'.


Beran dai ya fado akan cinyar wani wakilin jaridar NBC ne
dake fadar shugaban kasar mai suna Peter Alexander, da
misalin karfe 10:45 na safe.


Wasu daga cikin 'yan jaridar sun ranta ana kare, yayin da
wasu kuma suka yiwa beran tara-tara domin su kama shi.
Beran dai ya shiga ta wata kofa ne ya gudu abinsa, inda
masu kaman shi din suka hakura bayan ya bace musu.
An dinga sanya hoton wannan bera a kafar sadarwa ta
zamani, inda ya zama abin magana ga mutane.


Beraye, gafiyoyi, da kyankwaso dama sun jima da cika fadar
shugaban kasar, domin kuwa a shekarar da ta gabata wani
bera ya samu shiga fadar shugaban kasar, abinda ya saka
aka sanya masu korar beraye a kowanne mako a fadar
shugaban kasar.

No comments:

Join our WhatsApp group

Join our WhatsApp group
Latsa nan domin shiga group din mu na whatsapp
Powered by Blogger.