KU YI HAKURI NAN BADA DADEWA BA ZA'A DAINA DAUKE WUTA A NIGERIA, CEWAR SHUGABA BUHARI

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ba yan
Najeriya tabbacin samun wutar lantarki mai
dorewa kuma cikin sauki nan ba da jimawa ba.

Da yake magana a ranar bikin yanci na 59 a
ranar Talata, 1 ga watan Oktoba, Shugaban
kasar yace gwamnatinsa ta yanke shawarar
kawo sauyi a ma’aikatar wutar lantarki.


Yayinda tallafin kudin lantarki a gwamnatin
Buhari ya doshi naira triliyan 1.5 cikin shekaru
biyar, wutar lantarki da ake ba gidajen yan
Najeriya ya kasance kasa da megawatts 5,000.

“Muna shirin sauya harkokin ma’aikatar wutar
lantarki. A watan Agusta na wannan shekarar,
Mun kaddamar da shirin Shugaban kasa akan
wutar lantarki domin zamanantar da kasar a
rukuni uku: farawa daga 5 Gigawatts zuwa 7
Gigawatts, sai 11 Gigawatts a 2023, sannan
daga karshe 25 Gigawatts bayan,” inji Buhari.


A halin da ake ciki, shugaban kasar yace
jagoranci nagari da bunkasar tattalin arziki ba
za su tabbata ba tare da zaman lafiya,
ingataccen tsaro da kuma aminci a kasa. Yace
dole ne a yabawa dakarun sojin Najeriya da ke
ci gaba da sadaukar da rayukansu domin kare
martabar kasar nan wajen yakar kungiyar masu
tayar da kayar ta Boko Haram a tsawon

shekaru hudu da suka gabata.

No comments:

Join our WhatsApp group

Join our WhatsApp group
Latsa nan domin shiga group din mu na whatsapp
Powered by Blogger.