MAGANIN ZAZZABIN TYPHOID DA MALERIA CIKIN GAGGAWA NA GARGAJIYA SANGA-SANGA KO RAI DORE


Assalamu Alaikum
Yau zamu yi magana ne dangane da abinda ya shafi zazzabin
Typhoid, yanda ake kamuwa da shi, da yanda za a magance
sa.


Zazzabin Typhoid wani ciwon ne mai wuyar sha'ani, da ake
daukarsa ta kwayoyin Bacteria mai suna Salmonella typhi. Anfi
samun wannan ciwon akasashen masu tasowa. Kungiyar
Lafiya ta duniya ta kiyasta cewa mutune miliyan 22 ne a duniya
ke fama da wannan zazzabin na Typhoid, haka kuma mutun
200,000 sukan rasa rayukan su akowace shekara.


ME KE KAWO ZAZZABIN TYPHOID?
Bincike ya nuna ana kamuwa da wannan cutar ta hanyar wasu
kwayoyin halitta da ake kira salmonella typhi wayanda ake
samun su ta hanyar gurbataccen ruwa, ko abinci marar
tsabtaa. Ayayin da mutum yaci wani abinci ko wani abin sha
mai dauke da wannan kwayoyin cuta to sukan tafiya zuwa yan
hanjin mutum daga nan kuma sai su watsu zuwa cikin jinin
mutum inda zasu sami damar yaduwa zuwa hantar mutum da
kuma wasu sassa na jikin dan adam daga nan kuma sai su
cigaba da hayayyafa.
Bincike ya nuna cewa ba daga shigar kwayoyin cutar suke
haddasa ciwo ba, sukan dauki sati daya zuwa biyu kafin
mutum ya fara ganin alamomin ciwon su bayyana a gareshi.


Also read: WASU YAN MATA UKU SUNYI WA SAURAYI SHEGEN DUKA BAYAN SUN GANO YANA SOYAYYA DA SU, SU DUKA A BOYE


ALAMOMIN ZAZZABIN TYPHOID

CIWON KAI: Mutun zai rika fama da ciwon kai akoyaushe,
wani ko ya sha magani baya sauka, wani yakan sauka na dan
lokaci, kafin ya dawo.


CIWON CIKI: Yawan ciwon ciki alama ce da ke nuna mutun ya
kamu da zazzabin typoid, zaka samu kanka da murdawar ciki,
wani lokaci har da ciwon mara, zaka ji hanjin ka na kuka wani
lokaci har sai mutun ya ziyarci bayi da sauran su.


RASHIN KUZARI: Mutun zai kasance akoyaushe ba shi da wani
kuzari, aiki kadan zai yi sai gajiya.
Rashin jin dadin abinci yana daya daga alamomin kamuwar
cutar typhoid
Masana maganin gargajiya sunyi gwaji akan yanda ganyen
sanga sanga ke maganin zazzabin typooid.
Za asamu ganyen sanga sanga a wanke sa da ruwa masu
tsabta, atafasa sa. Bayan an tafasa za a sauke a tace ganyen
in ya huce a maida su ruwan sha.
Akan daka ganyen sa a tace ruwan ba tare da an tafasa ba.
Akan yi kunu da shi ana sha, ana kuma iya dafawa arika suraci
da wanka da shi.
Bayan  maganin ciwon typhoid da sanga sanga ke yi, bincike ya
nuna cewa sanga sanga yana kashe kwayoyin
plsmodium musamman falcifarum dake kawo zazzabin malaria
na cizon sauro wato dai baya ga kasancewa sanga sanga na
maganin typhoid to kuma yana maganin malaria.



RIGAKAFI.
Mu kula da tsabtace muhallin mu, musanman ruwan shan mu,
da kuma abincin mu. Mukan iya tafasa ruwan mu na sha kafin
muyi amfani da su, wannan hanya ce sosai da za ta taimaka
wurin rage yaduwar wannan ciwo. haka kuma rage cin abincin
sayarwa Wanda ba a tabbatar da tsabtar sa ba.
Allah ya bamu lafiya yasa mu dace.

No comments:

Join our WhatsApp group

Join our WhatsApp group
Latsa nan domin shiga group din mu na whatsapp
Powered by Blogger.