ZA'A GURFANAR DA MALAMAN MAKARANTAR ISLAMIYA TA RIGASA WACCE AKE DAURE ƊALIBAI



Rundunar ‘yan sandan jahar Kaduna ta
ce ta kammala bincike kan makarantar nan ta Rigasa wadda
aka ga yara a daure kuma za ta gurfanar da malaman
makarantar a gaban kotu.


Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jahar Kaduna,
DSP Yakubu Sabo Abubakar, ya ce duk da yake gwamnati ta
damka yaran makarantar ga iyayensu, akwai yiwuwar gayyato
wasu iyayen gaba kotu.

DSP Sabo ya kuma kara da cewa duk iyayen da suka nuna suna
sane da azabtar da yaransu a makarantar za’a tuhume su da
laifi, amma wadanda ba su san abun da ke faruwa ba sai dai su
ba da sheda gaban kotu.

Ita ma kwamishinar harkokin mata da walwalar al'uma ta
jahar Kaduna, Hajia Hafsat Mohammed Baba, ta ce gwamnati
ta dauki damarar bincike inda tuni aka rufe makarantar.

Shi ma babban daraktan hukumar kula da harkokin addini a
jahar Kaduna, Sheik Mohammad Jamilu Abubakar Albani, ya
ce gwamnati na da tsari kan makarantun addini amma za ta
kara tsaurara wadannan matakai.

No comments:

Join our WhatsApp group

Join our WhatsApp group
Latsa nan domin shiga group din mu na whatsapp
Powered by Blogger.