YA NEMI KOTU TA RABA AUREN SU IN BA HAKA BA YAYI RANTSUWA SAI YA FADA RIJIYA YA MUTU

Azeez, ya nemi kotun garajiya da ke zamanta a yankin Mapo na garin Ibadan a jihar Oyo da ta raba aurensa da matarsa, Mujidat, bayan shafe tsawon shekaru arba'in suna tare. 


Azeez ya yi barazanar cewa zai fada rijiya idan kotun bata amince da bukatarsa ta neman raba auren ba, saboda fusata shi da ya ce Mujidat na yi koda yaushe. Da yake fada wa alkalin kotun, Mista Ademola Odunade, irin mawuyacin halin da ya tsinci kansa, Azeez ya ce ya gaji da matsalolin matarsa da kuma irin barazanar da take yi wa rayuwarsa. Azeez, mai shekaru 70, ya ce bai taba samun farin ciki da jin dadi a cikin aurensa na tsawon shekaru 40 da ya yi da Mujidat ba, ya ce bayan bakin ciki da kuncin rayuwa babu abin da zai adar a zamansa da matarsa.


"Fiye da shekaru 20 kenan yanzu mu na rayuwa irinta mage da bera a tsakanina da Mujidat, don bata da ladabi ko kadan, na yi nadamar aurenta. "Tun da ta fahimci al'amura sun sauya min, babu kudi a hannu na, ta fara kawo min raini tare da kuntata min.

“Har 'ya'yan mu da muka haifa ta fada musu cewa ni ba komai bane, yanzu sun raina ni, saboda ko gaishe ni basa yi. "Yanzu an shafe fiye da shekara guda kenan da Mujidat ta tattara kayanta ta bar gida na. "Idan wannan kotu bata raba aurenmu a yau ba, na gwammaci na je na fada a cikin kogin 'Dandaru'," a cewar Azeez. Sai dai, Mujidat ta musanta wasu daga cikin zarge-zaregen da Azeezat ya yi mata tare da rokon kotun da kar ta raba aurensu, ko don saboda 'ya'yan da suka haifa. Da yake yanke hukunci, alkalin kotun ya raba auren tare da bayyana cewa alaka tsakanin ma'auratan ta yi lalacewar da ba zata gyaru ba.

Odunade ya bukaci Azeez ya biya Mujidat N5,000 a matsayin kudin da zata biya domin kwashe sauran kayanta da ke gidansa

No comments:

Join our WhatsApp group

Join our WhatsApp group
Latsa nan domin shiga group din mu na whatsapp
Powered by Blogger.