MAHAIFINTA YA TSINE MATA ALBARKA YACE BA SHI BA ITA SABODA TAKI AMINCEWA DA AUREN DOLE

Hawaye na gangarowa daga idanunta, cikin murya mai
sarkewa Ladidi (ba sunanta na asali ba)ta bayyana min
labarinta.

"Ana gobe daurin aurena, na je na sami babanmu na ce ya ba
ni kudi zan je lalle sai ya ce ai ban da ni za a daura wa aure.
Daga baya da adddare sai ya kira ni ya ce in shirya gobe zamu
je a yi min test (gwaji) domin za a daura min aure da wani.


"Ni kuma bana son sa, sai Ummata ta goyi bayana muka je
wajen Hisba aka warware auren" in ji Ladidi.
Ladidi, mai shekara 16 ta kasance kamar ko wace mace a
yankunan karkara a arewacin Najeriya, wato tana fara tasawa
aka fara yi mata maganar aure.


Masoya sun yi mata ca, kuma ta fitar da mutum daya da take
so ta aura- iyaye suka shiga maganar har aka sa ranar aure.
Amma kwana guda tal kafin a daura auren, sai mahaifin Ladidi,
Malam Ali ya sauya shawara, ya ce ya fasa bayar da ita ga
wanda ta fitar kuma ya yi mata sabon zabi- hukuncin da Ladidi
ta yi fatali da shi kamar yadda ta shaida min.


Ladidi da mahaifiyarta sun garzaya ga Hukumar Hisba ta jihar
Jigawa da ke arewacin Najeriya don ta sa baki a lamarin.
Hukumar ta saurari korafin Ladidi kuma ta kira Malam Ali
domin a yi maslaha a lamarin.
Daga karshe mutumin da aka aura wa Ladidi ya sake ta bisa
umarnin hukumar Hisba.


Sai dai mahaifin Ladidi ya musanta kalaman 'yarsa.
Ya ce ana saura kwana 15 a daura auren Ladidi mahaifiyarta ta
sauya magana, ta ce ba ta son Ladidi ta auri mijin da ta fitar.
Ya kuma ce ta yi haka ne domin tana so Ladidi ta auri wani
dan uwanta.


Lokacin da ya kamata ya zamo na farin ciki ga Ladidi ganin an
raba ta da wanda ba ta so, ya zama na kunci da fargaba.
Domin kuwa mahaifinta ya yi furucin da zai jefa ko wane da a
kunci, wato ya tsine mata.
"Duk abin da nai mata daga cikinta zuwa yau ban yafe mata
ba. Na ce ta je ta auri duk wanda take so. Kuma na sake
daukar mataki na ce duk 'yan uwa na ba wanda zai je daurin
auren," a cewarsa.


Hukumar Hisba

Hukumar Hisba wacce ke aiki da dokokin addinin musulunci,
kan yi ruwa ta yi tsaki a irin wadannan lamurra na rashin jituwa
tsakanin iyaye da 'ya'yansu dalilin aure.
A tsakanin wasu al'ummomi na arewacin Najeriya, ana kallon
mutuwar aure a matsayin wani abin assha musamman idan
mace ce ta nemi saki.

Sau da yawa, matan da aurensu ya mutu kan fuskanci
tsangwama a tsakanin al'umma wani lokaci ma daga danginsu
kamar yadda ya faru da Ladidi.

Malam Ibrahim dahiru Garki, kwamandan Hisba na jihar Jigawa
ya ce suna ganin irin wadannan matsalolin da dama.
"A cikin shekaru hudu mun yi wa mata a kalla 9821 sulhu
tsakaninsu da iyayensu da kuma tsakaninsu da mazajensu,
amma wanda aka yi wa tsakaninsu da mazajensu sun fi yawa"
a cewarsa.

Ya kuma ce kafin a kafa hukumar a jihar, matan da suka kashe
arensu musamman dalilin auren dole kan fada halin ha'ula'i.
Ya ce "sai ka ga yarinya ta shiga karuwanci, ko ma ta kashe
kanta. Amma a yanzu hukumar Hisba na shigowa ta tabbar an
samu maslaha."

Malam Ibrahim ya bayyana cewa hukumar Hisba ba ta raba
aure, illa dai ta yi sulhu. Sai dai wani lokaci ta kan mika
lamarin ga kotun addinin musulunci domin yanke hukunci.

No comments:

Join our WhatsApp group

Join our WhatsApp group
Latsa nan domin shiga group din mu na whatsapp
Powered by Blogger.