IKON ALLAH KAHO IRIN NA SHANU YA FITO MA WANI MUTUM DAN KASAR INDIA A TSAKIYAR KAI

IKON ALLAH KAHO IRIN NA SHANU YA FITO WA WANI MUTUM DAN KASAR INDIA A TSAKIYAR KAI

Kaho mai tsawon inci hudu ya fito ma wani mutum dan kasar Indiya mai shekaru 74, Shyam Lal Yadav, bayan ya ji rauni a kai cikin shekarar 2014. 



A kwanan nan ne Likitoci a asibitin Bhagyoday Tirth da ke birnin Sagar, Indiya suka cire kahon daga kan Yadav. Yadav, wanda ya kasance manomi daga kauyen Rahli da ke Madhya Pradesh, yaji rauni a shekarar 2014 a kansa inda hakan yayi sanadiyar tsirowar kaho a kan nasa, Daily Mail ta ruwaito. Tsiron wanda a kasafai akee ganin irinsa ba ya fi fitowa mutanen da shekarunsu ya jawato tsoffi.

Tsawon shekaru da dama Mista Yadav na ta aske tsiron, har sai da abun ya fara girma ba kama hannun yaro sannan manomin ya nemi ayi masa tiyata.

Kaho mai tsawon inci 4 ya fito a kan wani mutum bayan ya yi hatsari Source: Twitter Wani likita, Dr Vishal Gajbhiye, wanda ya yi masa tiyatan yace, "Kimanin shekaru biyar da suka gabata mara lafiyan ya ji rauni a kansa wanda daga bisani ya fara tsirowa. da fari, ya yi wasti da hakan tnda baya damunsa. sannan ya kan je wajen wanzamai su yanke masa.

"Amma lokcin da tsiron yayi karfi sannan ya ci gaba da girma, sai ya tunkari asibiti a Sagar." Gajbhiye ya bayyana cewa yayinda ake iya cire tsiron, akwai bukatar kula da halin da kasan ke ciki. yayinda aka yanke tsiron, har yanzu likitoci basu san abunda ya haddasa shi ba

No comments:

Join our WhatsApp group

Join our WhatsApp group
Latsa nan domin shiga group din mu na whatsapp
Powered by Blogger.