WATA MATA TA FADA TARKON MALAMIN DUBA INDA YA DAMFARETA NAIRA MILLION 11


WATA MATA TA FADA TARKON MALAMIN DUBA INDA YA DAMFARETA NAIRA MILLION 11


Hukumar 'yan sandan birnin tarayya sun kama wasu 'yan
duba 4 da laifin damfara
- Sun damfari wata mata har Naira miliyan 11 bayan sunce
sun hango mata daukaka
- Matar ta sanar musu yadda basa zaman lafiya da mijinta
don haka take da burin finsa kudi
A ranar Alhamis ne hukumar 'yan sandan birnin tarayya ta
cafke 'yan duba hudu da laifin damfarar wata mata miliyan 11.
Kehinde Ayoola mai shekaru 37, Sesan Fatoye mai shekaru 30,
Shola Samuko mai shekaru 50 da Seyi Fagbemi mai shekaru
32, sunce sun damfari matar ne bayan sun sanar da ita hango
mata daukaka da suka yi.


Wacce aka damfarar ta bi masu damfarar ne har inda suke da
burin haskawar rayuwarta nan gaba.
Mataimakin kwamishinan 'yan sandan birnin tarayyar, DCP
Sunday Babaji yace: "Yan sanda sun kamo 'yan duban ne bayan
da rahoton damfarar da suke yi ya isowa hukumar. A koken
wacce suka damfarar, tace sun damfareta Naira miliyan 11
kafin ta sanar da 'yan sanda."


"Wajen aikin nasu na Waru, Pyakassa da kauyen Galadimawa.
A yayin da hukumar ke kokarin kama sauran 'yan kungiyar, ana
shawartar mutane da su kiyayi mutanen da kan taresu a hanya
a matsayin 'yan duba."


Abubuwan da aka samu a wajensu sun hada da: Layu,
magungunan gargajiya, kwarya, kyallaye farare da jajaye da
kuma kwalabe.
A yayin da Kehinde Ayoola mai shekaru 37 daga jihar Ekiti ke
bayyana yadda suka damfari matar: "Nazo Abuja a shekarar da
ta gabata don siyarda magungunan gargajiya amma yanzu gani
a ragar 'yan sanda akan damfara."


"Na sanar da ita na hango daukaka tare da ita kuma zan
taimaketa wajen samunta. Ta yarda da zantuka na, don haka
ina isa gida na ba oga na waya ya kara mata gamsassun
bayanai. Ya umarceta da ta siyo bible da sauran abubuwa."
"Lokacin da tazo wajen aikinmu, mun sa ta rubuta abubuwa
uku da take so. Tace tana son tayi kudi, ta daukaka kuma tayi
suna. Tayi korafin cewa basa jituwa da mijinta don haka tana
son tafi shi kudi."


"Da abubuwan da ta lissafo, sai muka fara aiki. Mun bukaci ta
siyo akuya don ayi yanka. Bayan yankan sai muka ce muna
bukatar giwaye 4."
"Ta bada Naira miliyan 1.6 tunda munce mata duk giwa daya
N450,000 ake siyarwa. Bamu siyo giwa ba muka raba kudin
tsakaninmu."


"Bayan nan ne muka bukaci naira miliyan 9. A satin da ya
gabata ne ta kiramu akan karbar kudin. Daga zuwana 'yan
sanda suka cafkeni."

No comments:

Join our WhatsApp group

Join our WhatsApp group
Latsa nan domin shiga group din mu na whatsapp
Powered by Blogger.