KALAMAN SOYAYYA 10 MASU SOSA ZUCIYAR 'YAN MATA NA SAMARI

KALAMAN SOYAYYA 10 MASU SOSA ZUCIYAR 'YAN MATA NA SAMARI





KIN ZARCE SAURAN MATA.
Ina neman wata kalma wadda babu wanda ya
santa. Ina neman wata kalma da zan furta miki
cewa…..ke ta daban ce, ke kyakkyawa ce, kin
zarce sauran mata. Zuciya ta da taki ba za su
ta6a rabuwa ba har abada. Ina son ki.


SINADARIN RAYUWA TA.
SO shi ne abun da ya dun’kule zuciyoyinmu
waje guda har muka tsinci kanmu a cikin
soyayya, ina fatan ba za ki bari wani d’an
‘karamin abu ya zo ya raba tsakaninmu ba?
Ina son ki. Ke tamkar gishiri ce a cikin rayuwa
ta, idan na rasa ki zan yi rayuwa ne da babu
armashi a cikinta. Ki Huta Lafiya.


ZAN SO KI JI.
Da akwai wasu tarin tsintsaye da suke wuni
suna tattauna batutuwa a kan irin matsayin da
na baki a cikin zuciya ta. Zan so ki ji irin abun
da suke cewa, domin kuwa a lokacin ne za ki
tabbatar da irin son da nake yi miki. Ina Son
Ki!


KE CE MURMUSHI NA.
Da akwai miliyoyin furanni a cikin lambun
masoya a wannan duniya. Da a ce zan tsunko
kowanne fure na baki shi a hannunki, hakan
bai isa ya bayyanar da adadin yadda nake son
ki ba. Ke ce murmushi na, kuma ke ce farin-
ciki na. Ina Son Ki.


SONKI NA MOTSAWA A ZUCIYA TA.
Da akwai wasu lokuta da nake zubar da
hawaye saboda ke, na san za ki ce saboda
me?…..Da akwai wani lokaci da yake zuwa na
ji tamkar na yi fikafikai na tashi sama…..Kin
kuwa san duk saboda mene ne? Saboda
motsawar sonki a cikin zuciya ta da tsintar
kaina a cikin matsanancin shau’ki a dukkan
lokacin da na ji muryarki ko na tina da ke…..Ina
fatan za ki amince mu rayu a tare har abada.
Ina Son Ki!


HMM!! KI YARDA DA NI.
A dukkan lokacin da dare ya yi, ki d’aga kanki
sama ki kalli sararin samaniya, za ki ga wani
tauraro yana saukowa izuwa gare ki, karda ki
yi mamakin me ya sa haka ya faru? Ki yarda
da ni, hakan zai iya faruwa a zahiri domin
kuwa ni ma na yi hakan har ta kai ga na same
ki. Hmm! Ki Huta Lafiya.


INA SON KASAN
CEWA A TARE DA KE HAR ABADA.
A lokacin da na samu soyayyarki sai na ji
tamkar ni ne na fi kowa sa’a a duniya. A
dukkan sanda na rintse idanuwa na sai na
hango ni tare da ke muna tafiya a bisa
gajimare. Idan na kwanta bacci sai na yi
mafarkin mun zama mata da miji. Ina sonki,
tare da son kasancewa a tare da ke har
abada. Ki Huta Lafiya.


A CIKIN IDANUWANKI AKWAI WANI SIRRI.
Sama cike take da taurari masu hasken da ke
haske duniya a cikin kowanne dare. Amma
haske mafi haskaka fuska da yaye duhun
zuciya, na gan shi ne a cikin idanuwanki. Ki
Kula Min Da Kanki. Ina Son ki.


HARSHEN ZUCIYA.
Furanni na furta kalmomin yabo a kanki a
dukkan lokacin da na shiga lambu mai d’auke
da ‘korama gami da korayen ciyayi da bishiyu
masu d’auke da tsintsaye. Sukan rera baitukan
yabo a gare ki, cikin harshen da zuciya ce
kawai ke iya fahimtarsa. Ina Son Ki.


BA ZAN IYA RAYUWA IDAN BA TARE DA KE
BA.
A mafarki da kuma a cikin soyayya babu abun
da ba zai iya faruwa ba. Ina son ki sosai hakan
ya sa nake ji tamkar ba zan iya rayuwa idan
ba tare da ke ba. Ba na fatan rasa ki a rayuwa
ta, domin kuwa a dukkan lokacin da na rasa ki,
na tabbatar da rayuwa ta za ta shiga garari.
Ina Son Ki kuma ba zan ta6a canjawa a kan
hakan ba.

Rubutub Abba Muh'd Dan Hausa

No comments:

Join our WhatsApp group

Join our WhatsApp group
Latsa nan domin shiga group din mu na whatsapp
Powered by Blogger.