WANI DALIBI YA SAKA ALLURA A CIKIN MAFITSARARSA DON TA TAYAR DA SHI YAYI KARATU DA DADDARE


WANI DALIBI YA SAKA ALLURA A CIKIN MAFITSARARSA DON TA TAYAR DA SHI YAYI KARATU DA DADDARE


Wani dalibi da aka sakaya sunansa mai kimanin shekara 12
daga garin Shandi, a Gundumar Dian da ke kasar China, ya
fahimci cewa dabarar da zai iya yi wajen ya farka daga barci
don ya samu damar yin karatu cikin dare da sauran ayyukan
makaranta da aka ba shi ya yi a gida shi ya sa ya samu allura
mai tsawon santimita 10 ya zura a cikin mafitsararsa,

a cewarsa wannan ita ce kadai mafita.
Shi dai wannan matashi ya damu matuka a kan ya farka game
da abin da zai sa shi ya farka daga barci don ya yi nazarin
karatunsa, wannan yaro ya yi abin da ya bai wa kowa mamaki
saboda ganin yadda ya daukar wa kakarsa allurar da ake
amfani da ita wajen cire duk wani abu da ya makale a jikin
mutum sannan ya tura ta a cikin mafitsararsa.


Sai dai duk da
haka wannan dabara ba taimaka masa ya farka daga barcin
ba. A cewarsa mahaifiyarsa ce ta sa ya aikata haka, wannan
abu na da matukar wahala wajen fitar da ita cikin sauki, kuma
wannan ya sa ba ya iya tafiya kamar yadda ya dace
sakamakon radadin allurar da ya zura a jikinsa.


Mahaifiyar matashin ce ta fara fahimtar abin da yake faruwa,
saboda ganin yanayinsa ya sauya da yadda ta saba ganinsa,
tun a ranar 25 ga Yuli, yaron ya ki zuwa a wajen motsa jikin da
ya saba. Wannan ya sa mahaifiyar yaron ta yanke shawarar fita
da danta wajen motsa jiki saboda kwanakin da ya shafe bai yi
ba, daga nan ne ta fahimci cewa yana tafiya ne a hankali ba
kamar yadda ya saba yi ba.


Kafar sadarwa ta Asia Ona ta bayyana cewa mahaifiyar yaron ne ta yi
sanadiyar sanya yaron ya aikata hakan cikin fushi, a cewar
yaron wannan hanya ce za ta ba shi damar farkawa cikin dare
ya yi nazarin karatunsa.


Yaron, ya ce “A duk lokacin da zai yi nazarin karatunsa sai ya
fara barci, na yi abin da nake tunanin zai iya hana ni barci, don
haka na zura allura a cikin mafitsarata.”
Bayan mahaifiyar yaron ta ji abin da danta ya aikata ta razana
sosai, sai ta kai shi wani asibiti mafi kusa,


inda wani likita mai
suna Wang Shengding ya yi masa tiyata ya ciro allura daga
cikin mafitsararsa daidai kusa da abin da ke rike masa fitsari,
wanda hakan zai iya haifar masa da wani ciwo na daban ko ya
toshe masa wata hanyar jini.
Wang, ya kara da cewa, an yi nasarar ciro allurar mai tsawon
santimita 10 da take mallakin kakarsa ce ba tare da an ji masa
rauni ba.


Wannan rahoto wadansu dalibai da dama nata tafka
muhawara, inda wadansu ke kallon abin da yaron ya aikata a
matsayin karatun cike gibin da bai yi ba a baya don haka ya
fusata ya dage ya tabbatar da ya cika burinsa. A wani bangare
kuma wadansu na kallon abin a matsayin jahilci da kuruciya
ce tasa ya aikata haka.

No comments:

Join our WhatsApp group

Join our WhatsApp group
Latsa nan domin shiga group din mu na whatsapp
Powered by Blogger.