ALLAH DAYA GARI BAMBAM! WATA MATA TA NEMI A RABA AURENSU SABODA SON DA MIJINTA YAKE MATA YAYI YAWA


ALLAH DAYA GARI BAMBAM! WATA MATA  TA NEMI A RABA AURENSU SABODA SON DA MIJINTA YAKE MATA YAYI YAWA

Allah mai ik. A yayin da a wasu wuraren mata ke
korafin tursasawa da duka da zagi da rashin kyautatawa da
rashin nuna kauna daga mazansu, a Dubai da ke Hadaddiyar
Daular Larabawa, wata mata (da aka sakaya sunanta) ta kai mijinta
kotu tana neman ya sake ta, saboda ba ta jin dadin yadda yake
nuna mata tsananin kauna, musamman yadda yake ba ta
kyaututtuka da suka wuce hankali da kuma yadda a kullum
yake share gidansu kal-kal ba tare da gajiyawa ba.


Matar ta shaida wa Kotun Shari’a a Hadaddiyar Daular
Larabawa cewa mijinta yana nuna mata matsananciyar kauna,
ba ya yin musu ko gardama da ita, ba ya yi mata tsawa ko
kadan, maimakon haka sai dai ya yi ta nuna mata kauna da
tausayi, ga shi kuma kirkinsa ya wuce misali gare ta.

 Ta ce
wadannan halaye da mijinta yake nuna mata, su suka sanya a
kullum take jin bakin ciki da damuwa, don haka tana son kotu
ta raba auren su, domin ba za ta iya jure zama da mijin ba.



Matar ta shaida wa jaridar Khaleej Times cewa, “Kaunar da
yake nuna mini da irin tsananin jinkansa da kirkinsa gare ni
sun wuce iyaka, don haka ina son kotu ta raba aurenmu.”


Ta kara da cewa “Nakan ji bakin ciki iya wuya dangane da irin
kaunar da yake nuna mini. Yakan taimaka mini da share-share
a gida koda ban nemi ya taimaka ba.” Ta ce ko sau daya bai
taba kyararta ko ya yi mata musun wata magana ba, ga shi bai
taba daga mata murya ba da sunan fada a tsawon aurensu na
shekara daya.


Ta ce akwai lokacin da ta lura cewa kibarsa ta fara yawa, sai
ta yi masa korafi, inda nan da nan ya fara daukar matakan
rage kibar, ya rika cin abinci da magunguna na musamman na
rage kiba, sannan ya rika yin atisaye, kuma wurin yin hakan har
ya karye a kafa.


Matar ta ce, duk da cewa ya karye a kafa ya ci gaba da
kyautata mata, abin bai yi mata dadi ba, domin ta yi ta kokarin
ganin koda sau daya ne sun yi sabani ko cacar baki, amma
hakarta ba ta cimma ruwa ba. A cewarta, a duk lokacin da ta
saba masa, shi ne zai yi ta lallashinta, yana ba ta hakuri, yana
cewa ya yafe mata, sannnan ya biyo bayan haka da wata
kyauta ta mamaki gare ta.


“Ni ina matukar bukatar cacar baki da sabanin ra’ayi, amma ba
rayuwar salin-alin ba,” inji matar, kamar yadda ta shaida wa
’yan jarida.
Da kotun ta tuntubi mijin dangane da bukatar matarsa ta raba
aure, sai ya ce shi dai yana kaunar matarsa. Ya roki kotun da
kata ta raba auren.


Ya ce, “Ba daidai ba ne a ce za a raba
auren da aka daura tsawon shekara daya kawai. Akwai sauran
lokaci da ma’aurata za su ci gaba da zama, suna gyaran zama
daga kura-kuransu. Ni dai a kullum kokarina shi ne in ga na
kyautata wa matata, in ga na zama mai kirki da tausayi da
kauna a gare ta.”


Alkalin kotun ya dage shari’ar, sannan ya umarci ma’auratan
su koma gida su sasanta da juna.

1 comment:

  1. Hmm idan tukunya tace zatayi bori to jikinta zata bata.

    ReplyDelete

Join our WhatsApp group

Join our WhatsApp group
Latsa nan domin shiga group din mu na whatsapp
Powered by Blogger.