WANI BARAWO YA MUTU A JIKIN KARFEN WINDOW A LOKACIN DA YAJE SATA WATA MAJAMI'A

WANI BARAWO YA MUTU A JIKIN KARFEN WINDOW A LOKACIN DA YAJE SATA WATA MAJAMI'A

Wani matashi ya yi mumunar karshe bayan ya mutu
yayin da ya je sata a cikin Mujami'ar Prestige a
unguwar Arepo da ke yankin Awori cikin Abule Egba
a birnin Ikko watau Lagos ranar Talata.
Bayanai sun nuna cewa wannan barawo ya shiga
Mujami'ar ne da dare domin ya yi sata, amma sai
kanshi ya makale a karafan tsaro da aka sa a
Tagan Mujami'an, sakamakon haka ya shake har ya
mutu.


Rahotanni sun nuna cewa an taba yin sata har sau biyu a
wannan Mujami'a a bana inda aka dauke na'urar
sauti daga bisani kuma a sata na biyu aka sace
na'urorin lantarki.
Sakamakon haka ya sa shugabannin Mujami'an
suka yanke hukuncin sa karafan tsaro (burgler
proof) wanda kuma yin haka ya yi sanadin kamawa
tare da kashe barawon da ya addabe Mujami'an.

No comments:

Join our WhatsApp group

Join our WhatsApp group
Latsa nan domin shiga group din mu na whatsapp
Powered by Blogger.