NA GAJI DA MASIFAR NAN NIMA FICEWA ZANYI DAGA KANNYWOOD, CEWAR TEEMA MAKAMASHI

NA GAJI DA MASIFAR NAN NIMA FICEWA ZANYI DAGA KANNYWOOD, CEWAR TEEMA MAKAMASHI


kama Mawaki Nazir Ahmad Sarkin waka
jarumai da yawa sun fito sunyi Allah wadai da wannan abu da
hukumar tace fina-finai tayi
- Wannan yasa jaruma Teema Makamashi jakadiyar FKD ta
wallafa wani bidiyo inda ta nuna bacin ranta game da wannan
abu da yake faruwa a masana'antar
- Teema ta bayyana cewa ita ma za ta bi sahun abokanan
sana'arta da suka fita daga kungiyar saboda irin abubuwan da
suke faruwa a kungiyar
A irin kace nacen da ake ta faman samu dangane da kama
fitaccen mawakin nan Nazir Ahmad Sarkin wakar San Kano,
mutane da dama suna ta tofa albarkacin bakinsu dangane da
wannan lamari da ya faru da mawakin.
Wannan dalili ne yasa Jaruma Teema Makamashi jakadiyar
FKD tayi wani bidiyo cikin nuna alhini inda ta nuna bacin ranta akan kama Nazir din da aka yi har ta yi ikirarin ita ma ta kusa
tabi sahun abokanan sana'arta da suka fice daga kungiyar
shirya fina-finai ta Kannywood saboda ta gaji da abinda ke
faruwa a masana'antar.
Ga abinda jarumar ta ce:
"Assalamu Alaikum, kamar dai yadda kuka sani sunana Teema
Makamashi, yau kuma da abinda Kannywood ta wayi gari dashi
kenan, ni sai yau nake ji wai an kama Nazir Sarkin waka,
shugaban hukumar tace fina-finai a yiwa Nazir Sarkin waka

adalci a sake shi.


"Wannan abu da ake yi ko ba dan siyasa bane za ace saboda
siyasa ne, saboda mun zo mun shiga siyasa mun zake, sun zo
sai raba kawunan mu suke su suna can suna samun kudade,
mu munzo wajen da muke cin abinci a nan za a tsaya kullum
ana fada, babu ranar da garin Allah zai waye ba ayi wani abu a Kannywoodba.


"Wallahi gaskiya na kusa na bar Kannywood, ba zan iya
wannan masifar ba, a yiwa Nazir Sarkin Waka adalci a sake
shi, duka 'yan kwankwasiyya ake ta kamawa, 'yan APC din basa
laifi ne, tunda aka fara wannan abun ba a taba kama dan APC
ba, an jera hotunan jarumai biyar ance za a kamasu, kuma duk
'yan PDP ne."
Haka shima Jarumi Ali Nuhu ya fito ya roki hukumar da tayi
sassauci akan wannan lamari, inda ya roketa da ta yiwa

jarumin adalci ta sake shi.

No comments:

Join our WhatsApp group

Join our WhatsApp group
Latsa nan domin shiga group din mu na whatsapp
Powered by Blogger.