DAN SANDA YA KWANKWADI BARASA BAYAN YA BUGU YA SASARI JAMA'A MUTUM 9 SUN JIKKATA

Akalla mutane 9 ne suka samu munanan rauni sakamakon
sara da suka da suka samu daga wajen wani jami’in rundunar
Yansandan Najeriya daya debi barasa son ransa, ya sha ya yi
mankas abinsa!

Kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito wannan Dansanda mai suna Taiwo
Orisadare ya aikata haka ne a daren Juma’a a wani gidan
rawa dake garin Akuren jahar Ondo, kuma dansandan yana
aiki ne a ofishin Area Commander.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito wani shaidan gani da ido ya
bayyana cewa rikicin ya samu asali ne a lokacin da
Dansandan ya fara cin zarafin mutanen da suka shiga gidan
rawan, kuma a lokacin yana cikin halin maye.




“Ya fara marisa ne a lokacin, kuma baya saurara ma kowa a
gidan rawar, daga nan ne kawai sai ya zaro wuka yana sarar
mutanen da ita, ya yanki wannan ya soka ma wannan a haka
ya illata mutane 9, da kyar aka ci karfinsa.” Inji shaidan.


Shi ma wani da lamarin ya auku a gabansa kuma ya nemi a
sakaya sunansa ya bayyana cewa an garzaya da mutane zuwa
asibitoci daban daban dake garin Akure, sai dai yayin da wasu
suke warwarewa, wasu kuma suna cikin mawuyacin hali a
dalilin saran.


Da aka tuntubi kaakakin rundunar Yansandan jahar, Femi
Joseph don jin ta bakinsa, shi ma ya tabbatar da aukuwar
rikicin, kuma yace shi kanshi Dansandan ya samu rauni, kuma
yana samun kulawa a asibiti.

No comments:

Join our WhatsApp group

Join our WhatsApp group
Latsa nan domin shiga group din mu na whatsapp
Powered by Blogger.