UWA DA 'YA'YANTA BIYU SUN MUTU A LOKACI DAYA BAYAN SUNCI ABINCI MAI DAUKE DA GUBA

Wata uwa mai shekara arba'in da biyar da yaranta biyu sun
mutu a ranar Asabar bayan sun ci tuwon albo
wanda aka fi sani da tuwon Amala mai dauke da guba
a Odo-Ayedun Ekiti da ke karamar hukumar
Ikole na jihar Ekiti.


Shekarar babban dan nata 14 yayinda karamin
ke da shekara 12 a duniya.

An tattaro cewa mijin ne ya kawo garin albon
yayinda matar kuma ta tuka suka ci.
An gano dukkanin ahlin da suka ci abincin
kwance babu rai bayan sun kammala cin
abincin dare, illa mahaifin wanda ke cikin
mawuyacin hali a babban asibitin koyarwa na
rayya da ke Ido Ekiti.

Wata majiya da ta nemi a sakaya sunanta, tace
an tsinci gawawwakin wasu karnuka biyu da
suka ci guggubin garin a gidan.
An tattaro cewa makwabta wadanda suka shiga
alhini bayan gano lamarin sun sanar da yan
sanda.

Dan majalisa mai wakiltan Ikole II a majalisar
dokokin jiar Ekiti, Hon. Adeoye Aribasoye ya
tabbatar da lamarin ga manema labarai a ranar
Alhamis a Ado Ekiti.

Aribasoye ya kuma gabatar da lamarin gaban
majalisa inda yayi kira ga a binciki lamarin.
Da aka tuntube shi, jami’in hulda da jama’a na
rundunar yan sandan jihar, DSP Caleb
Ikechukwu ya tabbatar da lamarin.

Yace yan sanda za su hada hannu da sauran
hukumomi domin binciken abunda ya haddasa
mutuwarsu.

No comments:

Join our WhatsApp group

Join our WhatsApp group
Latsa nan domin shiga group din mu na whatsapp
Powered by Blogger.