INNALILLAHI... USMAN ALMAJIRI YAYI LUWADI DA YARAN UBAN GIDANSA MAZA SU 10 A SOKOTO

An kama wani almajiri da yake aiki a gidan wani mutumi yayi luwadi da 'ya'yan mutumin guda goma - Almajirin ya bayyana cewa shima tun yana dan shekara 5 a duniya wani mutumi ya koya masa wannan bakar al'adar ta neman maza -


Ya ce yana rokon hukuma ta sake shi, zai je yayi ta rokon Allah ya yafe masa duka laifukan da ya aikata Wani matashi mai shekara 21 mai suna Usman Abubakar, an kama shi da laifin yiwa yara kanana guda goma na maigidanshi luwadi, a Rungumi cikin karamar hukumar Sokoto ta Kudu, dake jihar Sokoto.



Abubakar dai da can almajiri ne kafin daga baya ya samu aiki a gidan maigidan na shi tsawon shekaru goma kenan da suka gabata. A wata hira da yayi da manema labarai, ya bayyana cewa wani mutumi ne mai suna Malam Muntari ya koya mishi kwanciya da mazan tun yana dan shekara biyar a duniya.


"Naje gidan shi nayi bara, sai yayi amfani da wannan damar yayi luwadi dani," in ji shi. Abubakar dai ya roki a yafe masa, inda ya ce: "Idan aka sake ni, zanci gaba da rokon Allah ya yafe mini dukkan abubuwan da nayi a baya." Shugaban rundunar masu yaki da safarar mutane, Barrister Hassan Tahir ya ce wanda ake zargin ya amsa laifinshi na kwanciya da 'ya'yan maigidan nashi guda goma. Ya ce wanda ake zargin za a mika shi gaban kotu domin ta yanke masa hukuncin da ya dace da shi.

No comments:

Join our WhatsApp group

Join our WhatsApp group
Latsa nan domin shiga group din mu na whatsapp
Powered by Blogger.