TURKASH! WANI DAN SHI'A YA FILLE KANSA DA WUKA YA MUTU HAR LAHIRA SABODA JIMAMIN ASHURA



Kasassabar wani mutumi ta ja masa tafiya lahira, yayin da yake baki ciki tare da alhinin
zuwan watan Al-Muharram na sabuwar shekarar Musulunci
na 1441 a kasar India, inji rahoton The Nation.


Kamar yadda jaridar Legit.ng ta ruwaito wannan mutumi dan Shia mai
suna Mohammad Sayum ya kashe kansa ne ta hanyar fille
kansa da kansa da wata zaftareriyar wuka daka hannunsa
yayin da yake wasa da ita, duk a cikin bakin cikin kisan
Hussaini, jikan Annabi Muhammad (SAW).


Wannan lamari dai ya faru ne lardin Nalanda, na yankin Bihar a
gabashin India, inda jama’a Musulman yankin su kanyi bikin
sabuwar shekarar Musulunci, sai dai ko da Sayum dan shekara
60 ya aikata ma kansa wannan aika aika, an yi gaggawar
garzayawa da shi zuwa Asibitin Sadar, amma ina, aikin gama
ya gama.


A duk shekara mabiya Shia suna gudanar da gangami don
nuna damuwarsu tare da alhinin mutuwar Imam Hussaini a
hannun Sojojin Kalifa Yazid a yakin Karbala wanda ya gudana
a shekarar 680 AD.


Daga cikin wannan gangamin alhinin da suke yi, su kan daki
jikkunansu, su shiga cikin garwashin wuta, yankan jikkunansu,
dukan kirji, marin fuska da dai sauran abubuwan nuna takaici
iri iri.


Ko a Najeriya ma mabiya Shia sun gudanar da kwatankwacin
wannan alhini, sai dai su basu kai ga yanka jikinsu ko kashe
kansu ba, amma dai sun gudanar da zanga zanga a garuruwa
daban daban, wanda hakan ya kawo rikici tsakaninsu da
Yansanda, har ta kaiga an yi asarar rayuka.

No comments:

Join our WhatsApp group

Join our WhatsApp group
Latsa nan domin shiga group din mu na whatsapp
Powered by Blogger.