ABUN KUNYA- KASAR GHANA TA MAKA NIGERIA DA KASA A GASAR IYA DAFA SHINKAFA DAFA-DUKA (JOLLOF)


ABUN KUNYA- KASAR GHANA TA MAKA NIGERIA DA KASA A GASAR IYA DAFA SHINKAFA DAFA-DUKA (JOLLOF)

A wani rahoto mai kama da al'mara da muka kalato a jaridar
BBC Hausa, mun samu cewa kasar Ghana ta yi kuli-kulin
kubura da kasar Najeriya a gasar iya dafa shinkafa dafa-duka
da aka gudanar a dandalin taro na Cressal Park da ke birnin
Accra.


Rahoton dai ya bayyana cewa, kasar Ghana ta lashe gasar iya
dafa shinkafa dafa-duka inda ta yi wa kasar Najeriya dauka
daya.
Wata mata da ake kira Madam Sika, ita ce ta lashe wannan
gasa inda ta samu kyautar zunzurutun kudi na wuri na gugar
wuri har dalar Amurka dubu biyu.


Babu shakka shinkafa dafa-duka wadda a turance ake kira
"Jollof Rice" , wani nau'in abinci ne mai farin jini da ya shahara
a kasashen nahiyyar Afirka da dama.


An dai shafe tsawon lokaci musamman a dandalan sada
zumunta ana adawa ta raha tsakanin Najeriya da Ghana a kan
wai wace kasa ce a cikinsu shinkafa dafa-dukarta ta fi dadi.


Mun samu cewa, baya ga fatan dorewar makamancin wannan
lamari a nan gaba, wadanda suka shirya gasar sun ce sun yi
hakan ne domin kyautata alaka tsakanin kasashen biyu.

No comments:

Join our WhatsApp group

Join our WhatsApp group
Latsa nan domin shiga group din mu na whatsapp
Powered by Blogger.