TA BA DUNIYA MAMAKI. WATA MATA YAR SHEKARA 40 TA HAIFI YARA 69 KAFIN TA BAR DUNIYA

A kasar Palastine an samu wata mata da ta haifi yara sittin
da tara a duniya Sai dai kuma matar ta mutu a lokacin da take da shekaru 40
a duniya bayan ta haifi yaran An bayyana cewa matar ita ce mace ta farko da ta fi
kowacce mace lafiya wajen haihuwa, amma kuma ba ita ce ta farko da ta fara haifar yara masu yawa irin wannan ba


Abin mamaki akwai matar da ta bar tarihi a duniya bayana ta
haifi yara sittin da tara. Wannan mata da ta haifi yara sittin da
tara dai 'yar asalin kasar Palastine ce. An ruwaito cewa ita ce
mace ta farko da ta kowa lafiya a bangaren haihuwa.

A cewar wani gidan talabijin na kasar Saudiyya dake kasar ya
bayyana cewa wannan mata dai 'yar kasar Palastine ta mutu
bayan ta cika shekara arba'in a duniya. Mijinta shine ya
bayyana hakan, inda yace matar tashi ta mutu.

A cewar wani rahoto na Guinness, ya ce matar ba ita ce ta
farko da ta fara haifar 'ya'ya masu tarin yawa irin haka ba a

wannan lokacin.

KARANTA KUMA:  HUKUMAR NSCDC TA KAMA WANI MAHAIFI DAKE LALATA DA 'YAR CIKINSA A JIHAR BORNO

A shekarun da suka gabata tarihi ya nuna cewa a kasar Russia
akwai wata mata mai suna Mrs. Vassilyeva matar wani
mutumi mai suna Feodor Vassilyev, ita ma an bayyana cewa
ta haifi yara 69 a haihuwa 27 da tayi.

A rahoton da muka samu na wannan mata 'yar kasar Russia
ya bayyana cewa ta haifi tagwaye sau goma sha shida (16)
wanda suka hada da 'yan hudu guda hudu da kuma 'yan uku
guda bakwai.

Likitan da yake duba matar ya bayyana cewa matar ta dauki
tazarar shekaru uku ba tare da ta sake haihuwa ba bayan

haihuwarta ta farko.

No comments:

Join our WhatsApp group

Join our WhatsApp group
Latsa nan domin shiga group din mu na whatsapp
Powered by Blogger.