IN DA RANKA: VIDEO: TSUNTSU YA RIKIDA YA ZAMA TSOHUWA TUKUF A JIHAR LAGOS

Wasu mazauna yankin Oworonshoki da ke jihar Lagas sun
shiga alhini ban al’ajabi bayan faruwar wani al’amari.
Sun je shafin Facebook inda suka yi ikirarin cewa wani tsuntsu
ya rikida ya zama tsohuwa. An tattaro cewa lamarin ya afku
ne ranar 21 ga watan Satumba.


Da suka wallafa video da hotuna domin tabbatar da ikirarin
wanda aka ce ya afku a gida mai lamba 39 a unguwar Miyaki
da ke Oworonshoki, masu amfani da shafin na Facebook
sunce tsohuwar ta tona cewa ta zo garin Lagas ne domin kai
wa wata mai ciki hari.

GA BIRIYON TSOHUWAR A KASA:

https://m.youtube.com/watch?v=Rxn5JKtcIOg





A wani labari na daban, mun ji cewa akalla kimanin shanu 36
mallakin wani makiyayi na Fulani sun halaka yayin da tsawa da
fada kansu a ranar Asabar cikin yankin Ijare na karamar
hukumar Ifedore ta jihar Ondo a Kudancin Najeriya.


An tattaro rahoton cewa, kiwon shanu da makiyaya na Fulani
ke yi a yankunan ya zamto wata mummunar al'ada da ke ci
gaba da haddasa rikici a kai a kai a tsakanin su da manoma
kamar yadda jaridar The Punch ta ruwaito.


Majiyar rahoton ta ruwaito cewa, makiyaya sun kada shanunsu
yankin wani jeji da ake kira Oke Owa, wanda ya kasance
haramtaccen wurin kiwo sai dai ga Sarakuna kadai sakamakon
tsarki da wurin yake da shi a fahimtar al'adu na al'ummar
yankin.

No comments:

Join our WhatsApp group

Join our WhatsApp group
Latsa nan domin shiga group din mu na whatsapp
Powered by Blogger.