TSOHUWA MAI KIMANIN SHEKARA 87 TA KASHE JIKANTA SABODA TUNANIN BA MAI KULAR MATA DA SHI BAYAN RANTA




Kamar yadda jaridar ABC ta ruwaito, wata tsohuwa
mai shekaru 87 a duniya mai suna Lilian Parks ta
bayyana dalilin da ya sanya ta kasha jikanta saboda
tana ganin cewa babu wanda zai kula mata dashi
bayan ranta.


A yadda rahoton ya bayyana, Joel, marigayin yana
zuwa ya zauna da kakar tashi kowanne karshe sati,
sannan a ranekun aiki kuma sai yaje zauna da
delibai ‘yan uwanshi. An gano gawarshi ne bayan
‘yar uwarshi taje ta duba shi a gidan kakarsu ranar
Lahadi dinnan da ta gabata.


Jami’an hukumar ‘Yan sanda na Bradenton sun
kama tsohuwar inda suka wuce da ita domin yin
gwaji a kwakwalwarta da kuma duba lafiyarta kafin
a kaita kotu a yanke mata hukuncin kisa. Kakakin
rundunar ‘yan sandan ya ce: “Wannan al’amari ne
babba ga jami’an mu.


Banu ji dadi ba kwata-kwata ace mutum yana
tunanin daukar ran wani saboda yana ganin ceza
idan babu shi ba zam somu kulawar da ta kamata
ba.” A cewar kakakin rundunar ‘yan sandan
Bradenton din, mahaifin Joel ya rasu, mahaifiyar shi
kuma tabi nesa da su.

No comments:

Join our WhatsApp group

Join our WhatsApp group
Latsa nan domin shiga group din mu na whatsapp
Powered by Blogger.