MUTUWA MAI BAN MAMAKI IYALAN GIDAN MUTUM DAYA SU 7 SUN MUTUM A LOKACI DAYA

Tsoro da fargaba ya cika ma zauna garin Mafoluku da ke
unguwar Oshodi a birnin Ikko watau Lagos da
safiyar yau, bayan an wayi gari an ga wani iyalin
mutum 1 su 6 tare da wata bakuwa duk sun
mutu.


Mai gidan tare da matarsa, da yaransu hudu har da
wata bakuwa mai dauke da juna biyu sun mutu
gabadayansu, bayan an gano haka da misalin karfe
10 na safiyar yau a gida mai lamba 19 da ke
unguwar Olowora.



Bayanai sun ce ana zargin cewa iyalin sun ci abinci
mai guba ne. An shaida wa jami'an yansandan
Makinde, kuma sun dauke gawakin mamatan daga
gidan.


No comments:

Join our WhatsApp group

Join our WhatsApp group
Latsa nan domin shiga group din mu na whatsapp
Powered by Blogger.