MASIFA DA BALA'I 13 GA MASU KALLON FINA-FINAN BATSA (BF) A DUNIYA DA LAHIRA MUDDUN BASU TUBA BA

MASIFA DA BALA'I 13 GA MASU KALLON FINA-FINAN BATSA (BF) A DUNIYA DA LAHIRA MUDDUN BASU TUBA BA



1- shin kun san abubuwan da kuke kallo yana daga cikin
manyan laifuka (kaba'ir ).

2- shin kun san abinda kuke kallo yana gadar da kaskanci da kuma raunin imani da lalacewar dabi'a ta kowane bangare.

3- shin kun san abinda kuke kallo yana kawo raunin idanu da kwakwalwa, da yawan mantuwa, abu kankani ma sai kana
kamantawa.

4- shin kun san wannan kallon yana sa mutum ya fita cikin wadanda Allah ya yarda dasu. Kuma yana rage kwarjini da
daraja.

5- Shin kun san wannan kallon yana hana mutum samun ilimi ko mantashi. Kuma yana toshe basira.

6- shin kun san wannan kallon yana hana samun jin dadin rayuwar aure mai inganci da mijinki ko matarka, kuma duk da
kuna son juna.

7- shin kun san cewa zaku iya mutuwa a cikin wannan yanayin aikin sa6o (wato kuyi mummunar cikawa). Kuma wanda ya
shaqu da kallon baya iya dainawa cikin sauki

8- shin kun san jikinku zai gaya muku ko badade ko bajima in baku tuba ba, don za'a ga mummunan sakamako a duniya da
lahira.

9- shin kun san duk abinda kuka yada maras kyau kuna da kason zunubi, in ko yai sanadiyyar lalacewar wani kuna da
zunubin koda kuna lahira.

10- shin kun san cewa duk wanda yabar wani abu domin Allah, Allah zai musanya masa da abinda ya fishi alkhairi. Don haka
ku daina don Allah.

11- shin kun san cewa Allah yana farin ciki sosai da tuban bawansa. Don haka ku tuba ku daina.

12- shin kun san cewa Allah zai wadataku da falalarsa idan kuka kame kawunanku gada haramun. Allah zai kara maku
kamala da nagarta.

13- shin kun cewa sha'awar yan mintina ta haramun zata jawo maku azaba a gobe lahira..

Allah ya tsare mana imanin mu da mutumcin mu yasa mu
gama lafiya.

No comments:

Join our WhatsApp group

Join our WhatsApp group
Latsa nan domin shiga group din mu na whatsapp
Powered by Blogger.