KAI DUNIYA: WATA MATA TA KASHE JARIRIYAR KISHIYARTA YAR KWANA 3 TA HANAYAR ZUBA MATA FIYA-FIYA A BAKI

Wata mata yar shekara 22, Harela Uba ta shiga hannun
Yansandan jahar Neja bayan ta shayar da jaririn kishiyarta
wanda bai wuce kwanaki 3 a duniya ba kacal gubar fiya fiya,
inda take ya zamto matacce, inji rahoton jaridar Blue Print.


Matar mai suna Harela ta aikata wannan ta’asa ne
a ranar 14 ga watan Satumba a gidansu dake kauyen
Shakodna cikin karamar hukumar Shiroro na jahar Neja, kuma
mijinta, Uba Saidu ne ya kai karar matarsa tasa da kansa ga
Yansanda.


Ita dai Harela wanda ita kanta tana dauke da ciki wata 8 ta
baiwa diyarta mai shekaru 7 fiya fiyan ne ta shayar da jaririn
kishiyarta, yayin da kishiyar mai suna Fa’iza Uba ta bar jaririn a
dakinta ta shiga cikin bandaki tana wanka.


KARANTA WANNAN: IKON ALLAH KAHO IRIN NA SHANU YA FITO MA WANI MUTUM DAN KASAR INDIA A TSAKIYAR KAI

Sai dai a lokacin da ta fito daga bandakin sai ta tarar farin
kumfa a bakin jaririn, a nan ta kwantsama ihu nan da nan aka
garzaya da jaririn zuwa asibiti, amma ko kafin a isa a asibitin
ya cika. Kaakakin Yansandan jahar, Mohammed Abubakar ma
ya tabbatar da aukuwar lamarin.


“Mun gayyaci uwargidar Malam Uba Saidu, Harela sakamakon
ita kadai ce a gida a lokacin da lamarin ya auku, domin mu yi
mata tambayoyi, a yayin da take amsa tambayoyinmu ne ta
tabbatar mana da cewa ita ta aiki diyar yar shekara 7 mai suna
Khadija da fiya fiya domin ta shayar da jaririn Fa’iza.” Inji shi.
Daga karshe kaakakin yace za su gurfanar da Harela gaban
kotu da zarar sun kammala gudanar da bincike.


A wani labarin kuma, Yansanda sun kama wasu mutane guda
7 daga cikin ‘Yan kwamiti’ da jami’an hukumar Hisbah da laifin
kashe wani mutumi mai suna Ibrahim A Ibrahim sakamakon
suna zarginsa da sace budurwarsa Maryam Salmanu dake
garin kontagora.

No comments:

Join our WhatsApp group

Join our WhatsApp group
Latsa nan domin shiga group din mu na whatsapp
Powered by Blogger.