MAHAIFIYATA TA TSINE MIN ALBARAKA SABODA NA KOMA ADDININ MUSULUNCI

Wata ma'abociyar amfani da dandalin sada zumunta na
Tuwita mai suna (@ayushadeyah) ta bayyana yadda ta koma addinin
Musulunci amma ta shafe tsawon shekaru 5 kafin ta sanar da
mahaifiyar ta


Ayushhadeyah ta ce mahaifiyata ta tsine mata a karo na
farko bayan ta kira ta domin sanar da ita cewa ta zama
Musulma
- A cewar matashiyar, daga baya mahaifiyarta ta zo ta hakura
bayan ta fahimci cewa babu abinda zai hana ta cigaba da
zama a cikin addinin Musulunci


Wata ma'abociyar amfani da dandalin sada zumunta na Tuwita mai lakabi da @ayushadeyah ta bayyana yadda ta koma
addinin Musulunci amma ta shafe tsawon shekaru 5 kafin ta
sanar da mahaifiyar ta.
A yawancin al'adun Afrika, mace na koma wa addinin mijinta
bayan sun yi aure, lamarin da yasa @ayushhadeyah ta iya rike
sirri na tsawon shekaru biyar ba tare da sanar da mahaifiyarta
cewa ta canja addini ba.


Matashiyar ya bayyana cewa ta kasa sanar da mahaifiyarta ne saboda tana tsoron yadda mahaifiyarta zata ji idan ta fada
mata. Ta kara da cewa amma daga baya wata kawarta ta bata shawarar cewa ta cire tsoro, ta sanar da mahaifiyarta gaskiyar

zance.

Ayushhadeyah ta ce mahaifiyarta ta ji matukar jin ciwon labarin cewa ta koma addinin Musulunci, musamman ma yadda ta
boye mata gaskiyar zancen har na tsawon shekaru biyar.
A cewar ta, "mahaifiyata ta ji matukar ciwon jin labarin, a cikin
kuka ta dinga yi min tambayoyin me tayi min da zan yi mata
haka tare da fada min cewa zan iya saka mata guba tunda har na iya boye mata maganar na canja addini na tsawon shekaru
biyar .''

Mahaifiyar matashiyar har tsine mata sai da tayi tare da yi
mata kashedin cewa kar ta sake cewa ita ta haife ta, amma,
matashiyar ta ce ta shaida wa mahaifiyarta cewa zata cigaba

da yin addinin duk da haka.

No comments:

Join our WhatsApp group

Join our WhatsApp group
Latsa nan domin shiga group din mu na whatsapp
Powered by Blogger.