KARSHEN DUNIYA: HUKUMAR NSCDC TA KAMA WANI MAHAIFI DAKE LALATA DA 'YAR CIKINSA A JIHAR BORNO

Hukumar tsaron cikin gida ta Najeriya NSCDC, ta cafke wani mahaifi mai shekaru 46, Muhammad Pantami, da laifin zakkewa diyarsa budurwa 'yar shekaru 15 a jihar Borno. 


Kwamandan hukumar NSCDC reshen jihar Borno, Abdullahi Umar, shi ne ya bayar da tabbacin wannan rahoto yayin ganawa da manema labarai a ranar Litinin da ta gabata kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito. Kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN ya ambato Kwamandan hukumar yana cewa, Pantami ya shiga hannu ne a ranar 29 ga watan Agustan da ya gabata cikin yankin Balabulin-Allajeri da ke wajen birnin Maiduguri.


Ya ce wata dattijuwa ce ta taimaka wa wannan budurwa wajen kai kokenta zuwa ga ofishin hukumar, lamarin da ta ce mahaifinta ya saba yi mata ta karfi wajen gurbata budurcinta na 'ya mace. A yayin da a halin yanzu hukumar NSCDC ke ci gaba da gudanar nazari a kan wannan lamari na Allah wadai, Ibrahim ya ce bincike ya tabbatar da cewa an keta haddin wannan budurwa babu adadi cikin shekarar nan da muke ciki.


Ya ke cewa, "wanda ake zargi duk da kasancewar yana da mata biyu, ya saba sulala wa dakin diyarsa inda ya ke keta mata haddi a yayin da take bacci. Ya fara aikata wannan mummunar ta'asa ne tun tana 'yar shekaru 14 da haihuwa". Ya kara da cewa, za a gurfanar da mahaifin wannan budurwa a gaban kuliya da zarar bincike ya kammala inda zai fuskanci hukunci kwatankwacin fasadin da ya aikata.

No comments:

Join our WhatsApp group

Join our WhatsApp group
Latsa nan domin shiga group din mu na whatsapp
Powered by Blogger.