KASH! FUSHI YA SA WANI MUTUM YA KASHE MAHAIFIYAR MATARSA DA KANWARTA DA DANTA JARIRI

Rundunar 'yan sandan Najeriya reshen jihar Edo ta kama wani
mutum mai shekaru 44 mai suna Edoghogho Omorogbe kan
laifin kashe surukursa, uwar matarsa da kanwar matarsa da wani jarriri dan
watanni shida.


Ya kashe su ne a ranar 10 ga watan Satumba a garin Iguadolor
a karamar hukumar Ovia ta Arewa maso Gabashin Jihar Edo
kuma an gano gawarwakin wadanda ya kashe wato Mrs Alice
Omorogbe 52, Mrs Blessinf Efe 25 da jaririn ta.


Edoghogho ya ce ya fusata ne ya kashe surukan nasa saboda
duk lokacin da ya samu matsala da matarsa su kan dauki
hayar matasa domin su lakada masa dukan tsiya.

"Ni direban tifa ne amma tunda damina ya kama na koma aikin
kwadago.

KARANTATASHIN HANKALI: AN CIRO COKULA (SPOONS) GUDA ASHIRIN DA HUDU A CIKIN MARAR LAFIYA


"Na kashe su ne saboda fushi da nayi domin suruka ta ta kan
dauki hayan matasa suyi min duka. Ta kan ce ina yi wa mata ta
magana. Idan na samu rashin jituwa da mata ta, za ta aiko
matasa suyi min duka.


"Ban san cewa adan zai taba jaririn ba. Na tsere bayan da na
kashe su. Daga baya na dawo na fadawa mahaifi na abinda na
aikata. Ban ga mata ta ba tun bayan da na kashe mahaifiyarta
da 'yar uwanta."


Kwamishinan 'yan sandan jihar, Danmallam Abubabakar ya ce
za a gurfanar da wanda ake zargin a kotu da zarar an
kammala bincike.

No comments:

Join our WhatsApp group

Join our WhatsApp group
Latsa nan domin shiga group din mu na whatsapp
Powered by Blogger.