WA'IYAZUBILLAH, WATA BUDURWA TAYI RIDDA TA FITA DAGA ADDININ MUSULUNCI ZUWA NA KIRISTA



Wata budurwa 'yar kasar Guinea tayi ridda daga addinin Musulunci ta koma addinin Kiristanci

- Budurwar ta bayyana cewa bayan komawrta iyayenta sun nemi ta bar musu gidansu ko kuma su saka a kasheta

- Ta ce hakan ya tilasta ta gudowa Najeriya inda yanzu haka take zaune a wata maboya yayin da 'yan sanda ke nemanta ruwa ajallo

Wata budurwa mai shekaru 20 Musulma 'yar kasar Guinea, mai suna Grace Koulibaly ta wallafa wani rubutu a shafinta na Facebook akan irin barazanar da take samu na kisa bayan komawarta addinin Kiristanci, inda hakan ya tilasta ta gudowa Najeriya daga kasar Guinea.

Budurwar wacce ta samu takardun zama a kasar Amurka ta koma addinin Kiristanci shekaru uku da suka gabata, inda ta ce iyayenta sun dawo kasar Guinea domin yin hutu, inda tayi zargin cewa sunyi hakan ne domin su tilasta ta komawa addinin Musulunci.

Latsa nan ka karanta: TO FA: WALLAHI SAI NA KASHE MAHAIFIYATA SANNAN NA KASHE KAINA, SABODA NA KAMATA DUMU-DUMU TANA ZINA DA SAURAYINA

Grace ta ce iyayen na ta sun dauke takardun zamanta na kasar Amurka, da kuma duka kudinta, kwanaki uku bayan zuwan su Guinea


Sai dai kuma bayan taki yadda ta koma addinin Musuluncin, iyayentasun bayyana mata cewa ko ta nemi hanyarta daban, ko kuma su saka a kasheta. Grace ta bayyana cewa yanzu haka tana nan ta boye a wani waje a Najeriya yayin da 'yan sanda suke nemanta ruwa ajallo domin mayar da ita kasar Guinea.

Ta bayyana cewa ita ce ta yanke hukuncin gudowa Najeriya babu wanda ya takura ta ko ya sato ta, Grace ta kara da cewa iyayenta sun kai rahoton cewa wani Fasto ne ya sace ta.

No comments:

Join our WhatsApp group

Join our WhatsApp group
Latsa nan domin shiga group din mu na whatsapp
Powered by Blogger.