HANYOYIN 10 DA ZAKA NUNAWA MUTUM KANA SONSA BA TARE DA KA FURTA MASA BA

A yau munzo muku da hanyoyin 10 da zaku nunawa mutum kuna sonsa ba tare da kun fada masa ba,  shi da kanshi zai gane hakan.




1. SATAR KALLO 
Ana iya amfani da satar kallo wajen fahimtar da mutum ana sonsa. Musamman ma kallo irin na soyayya, mafi yawanci anfi saurin ganewa idan ya kasance da zarar kun hada ido kayi sauri ka kau da kanka  baya gajiya da kallun ki. Idan kuna tare ki kula, abu kadan zaki yi, zai tsura maki ido, Haka kuma tausasa idon wurin Magana da wacce kake so, ta yadda idan ya kalli idonka zai ga tausayi da so a cikinsu




2. KASANCEWA A TARE
 kasancewa a tare,  ko nuna son kasancewa a tare na daya daga cikin alamomin da mutum zai gane ka kamu da sonsa,  ka ringa yawan bi ta wurin da zaka hadu da masoyiyarka, ka yawaita son magana da ita a waya ko a text, ka kasance tare da su a koda yaushe




3. TAUSASA ZANCE
Ka zama kana tausasa zance a duk lokacin da kake magana da wanda kake so,  ba dole sai maganar soyayya ba,  magana da fira mai dadi ana raha kawai ya isa ya aika musu da saqon soyayya




4. YARDA DA AMINCI
Nuna ka yarda da mutum ka amince masa ma hanya ce dazai nunawa mutum kana sonsa,  saboda yarda tana daya daga cikin manyan alamomin so,  ka ringa fadawa mutum sirrinka,  da wasu daga cikin abubuwan daya shafeka,  wannan ma na daya daga cikin alamomin so


5. YAWAN ZANCEN MUTUM
Yawan firar mutum,  musamman da abokansa ko kuma en uwansa dai wanda bazaka jima kunya ba,  wanda kasan kuma idan kayi musu maganar to zasu iya labartawa wanda kake so,  duk sanda kake tare da Kawar wacce kake so,  ka yawaita yi mata firar wannan a bar son taka.

KARANTA KUMA: DALILIN DA YASA MATAN HAUSAWA BASA IYA FURTA SOYAYYAR SU GA WANDA SUKE SO KO DA KUWA SUNA CUTUWA


6. KULAWA/DAMUWA
Ka ringa nuna ma wanda kake so kulawa sosai ta musamman,  wacce zata nuna mishi sosai ka damu dashi, musanman ta bangaren kulawa da al'amuransa da duk wani abu daya shafe shi.




7. KYAUTA
kyauta na taka muhimmiyyar rawa sosai wurin aika saqon dake a cikin zuciya,  kana son mutum?  Ka kasance cikin mishi kyauta akai-akai,  mace ko namiji,  'yan turarukan nan,  chocolates, cards,  da yan kyautuka dai masu sauqi haka, sannan idan macece,  banda daukar kiranta idan ta kira,  harkar Girma Alaji,  ka jira har kiran ya katse sai ka kirata,  zaka ga tana son kiranka sosai,  ko flashing bazata maka ba,  bama kamar in kana tura mata credit,  "na kiraka baka daga ba", "kawai bana son karar miki da kati ne" babbar harka kawai Alaji




8. YAWAN FIRAR SOYAYYA. 
Yawan yima abun sonka firar soyayya zai iya sakawa ya dauka alama,  ka ringa tsokano shi akan abunda ya shafi soyayyarsa,  ta haka kaima zaka iya kutso kai da naka kalaman soyayyar ba tare daka furta wannan kalmomin guda uku ba,  "Gaskia kin iya fira sosai, shiyasa idan kina magana bana so ki daina". 
"Na rasa dalilin da yasa ko me ya faru yana tunana mun ke ne"
 "Dadin hirarki ke sawa na kasa mantawa dake a duk irin yanayin da na tsinci kaina" Kalamai dai masu dadi da nuna kulawa

KARANTA KUMA: ALAMOMI 20 DA ZAKA GANE KA KAMU DA SON MUTUM


9. NUNA KISHI
Ba kuma irin na zakewa ba don ka ganta da wani ka kama fushi ba,  haba ka tsaya ka samu shiga dai tukun,  kin kirashi busy?  Ki dan shagwabe kina nuna mishi rashin jin dadinki,  ko late reply, ko kuma ka ganta tana magana da wani,  duk dai wani hanya da zaka nunawa mutum kana kishinsa.




10. TATTALI
ka ringa tattalin abin sonka sosai kana nuna mishi kulawa,  ka maida farin cikinsa naka,  damuwarsa ta zama taka,  inda hali ma karka bari ya shiga damuwar,  ka ringa tattalinsa sosai da sosai

No comments:

Join our WhatsApp group

Join our WhatsApp group
Latsa nan domin shiga group din mu na whatsapp
Powered by Blogger.