TASHIN HANKALI: AN CIRO COKULA (SPOONS) GUDA ASHIRIN DA HUDU A CIKIN MARAR LAFIYA

Wata tiyata da aka yiwa wani matashin saurayi dan shekara ashirin a duniya an ciro abubuwa sama da talatin a cikin shi, ciki kuwa hadda cokula guda ashirin da hudu


Wannan lamari dai ya faru a kasar Egypt ne a babban birnin Cairo, inda aka garzaya da matashin zuwa asibiti bayan ya fara korafin cikin shi nayi masa ciwo 

Likitan da ya yiwa saurayin tiyatar ya bayyana cewa matashin ya hadiye wadannan abubuwa ne tsawon watanni shida da suka gabata Wani abun mamaki da ya faru a birnin Cairo na kasar Egypt, yayin da aka kai wani matashin saurayi asibiti bayan ya fara korafi cewa cikin shi na yi masa ciwo. Abubuwan da likitocin suka samo a cikin shi sun bawa kowa mamaki. 

KARANTA KUMA: KASH! FUSHI YA SA WANI MUTUM YA KASHE MAHAIFIYAR MATARSA DA KANWARTA DA DANTA JARIRI

Shugaban likitocin Dr. Amjad Fouad ya bayyana cewa binciken da suka yi sun gano cokula da wasu abubuwa a cikin marar lafiyan. 

Matashin mai shekaru 20 ya samu matsalar tabin hankali. Bayan likitocin sun yi masa tiyata sai suka samu cokula guda ashirin, cokula masu yatsu guda hudu, zoben zinare, sarka da dan kunne da dai sauran abubuwa masu tarin yawa a cikin nashi. 

Yanzu haka dai an cire duka abubuwan a cikin marar lafiyan, kuma ya samu sauki. Yanzu dai tambayar da ake yi ita ce, ya aka yi duka wadannan abubuwa suka shiga cikin shi? 

A cewar likitan da yayi wannan tiyata, yace matashin ya hadiye wadannan abubuwan na tsawon watanni shida, yana kuma yawo da su a cikin shi na tsawon wannan lokacin.

 Haka ita ma mahaifiyar matashin ta bayyana cewa ita ma tayi mamaki yadda taga wasu abubuwa suna bacewa a wajen dafa abincinta, amma ba ta taba kawowa shine yake hadiyewa ba. 

No comments:

Join our WhatsApp group

Join our WhatsApp group
Latsa nan domin shiga group din mu na whatsapp
Powered by Blogger.