BABU ABINDA BUHARI YAYI WA NIGERIA BANDA JEFA TA CIKIN TALAUCI DA KUNCI, INJI SHEIKH ABUBAKAR GUMI

BABU ABINDA BUHARI YAYI WA NIGERIA BANDA JEFA TA CIKIN TALAUCI DA KUNCI, INJI SHEIKH ABUBAKAR GUMI




Shararren malamin addinin musuluncin
nan wato, Sheikh Ahmad Gumi ya ce zaben
2019 shi ne zabe mafi muni a tarihin
Najeriya, kasancewar a lokacin ne aka zabi
gwamnatin da bata tsinanawa jama’a komi
ba karkashin jagoranci Muhammadu
Buhari.


Sheikh Gumi ya daura laifin wannan
gwamnatin ne a kan manya-manyan ‘yan
siyasan kudancin Najeriya, inda ya ce babu
abinda gwamnatin Buhari ta yiwa Najeriya
in banda jefa mutane cikin talauci.


Majiyarmu ta samu daga Nijeriyarmu a
dadanlin facebook, ya wannan abu a
matsayin ganganci daga bangaren ‘yan
siyansan kudancin Najeriya, inda ya ce sun
marawa Buhari baya ne a zabukan 2015
da 2019 saboda wadansu bukata na kashin
kansu.


Sheikh Gumi ya furta wadannan kalaman
nasa ne a lokacin da yake karbar bakuncin
wani babban malamin addinin kirista, Isah
El-Buba wanda ya ziyarcesa a gidansa
dake Kaduna ranar Alhamis 19 ga watan
Satumba.


Gumi ya ce: “Zaben 2019 shi ne zaben da
yafi ko wane zabe muni da takaici a tarihin
Najeriya, saboda zabe ne wanda ya raba
kan ‘yan Najeriya a bisa jahilci da rashin
sanin ya kamata.


“Bukatar mu ita ce mu samu shugaba
wanda zai jagorance mu ba tare da nuna
bambanci tsakanin wadansu bangarori ba,
ina nufin wanda zai dauki dukkanin ‘yan
Najeriya a matsayin diyansa.


“Sai dai kuma kash akasin hakan ne
abinda muke fuskanta a yanzu. Kawunan
su rarrabu, ba kuma komi ya kawo
wannan ba sai matsanancin talauci. Duk
miyagun laifukan da ake aikata a yanzu
talauci ne ya kawo su.


“Yan siyasa su ne masu kawo wa kasar nan
matsala. Wai gwamnatin dake ikirarin yaki
da talauci kenan, sai ga shi an gano daya
daga cikin gwamnoninta yana cusa daloli
cikin aljihu. Babu abinda zai bamu cigaban
da muke bukata a kasar nan idan ba
sahihin zabe ba.” Inji Gumi.

1 comment:

Join our WhatsApp group

Join our WhatsApp group
Latsa nan domin shiga group din mu na whatsapp
Powered by Blogger.