MATASHI YA CAKAWA MAHAIFINSA WUKA YA KASHE SHI HAR LAHIRA A JAHAR KANO

Wani matashi mai suna Habibu Ibrahim ya caccakawa mahaifinsa mai suna Malam Ibrahim Salihu mai shekaru 80 wuka har lahira a kauyen Asada, karamar hukumar Doguwa ta jihar Kano. Amma a ranar Talata, jami'an yan sanda sun bayyana cewa sun damke Habibu bayan ya arce daga garin. 



Kakakin hukumar yan sandan, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce daya daga cikin yan uwan Habibu, Yahaya Ibrahim, ya kai kara ofishin hukumar dake Doguwa a ranar Lahadi, 15 ga Satumba, 2019 cewa kaninsa ya cakawa mahaifinsu wuka cikin dare. Ya ce: "Yayinda muka samu labarin, jami'an hukumar sun garzaya da shi asibitin Doguwa domin jinya amma ya mutu misalin karfe 6:30 na asuba."


 Kakakin yan sanda ya ce bayan gudanar da binciken da ya kamata kan gawar, an mika ta ga iyalan domin jana'izarsa bisa ga koyarwan addinin Musulunci. "Binciken da muka gudanar ya nuna cewa yaron dan kwaya ne kuma ya aikata wannan aika-aika ne bayan ya bugu da kayan maye." "Yan'uwansa sun bayyana mana cewa Habibu ya dade yana ta'amuni da muggan kwayoyi kuma hakan ya kasance babban kalubale ga mahaifinsu har ya kai ga rasuwarsa."


A cewar DSP Haruna A karshe, ya ce kwamishanan yan sandan jihar, Ahmed Iliyasu, ya bada umurnin mayar da bincikensa sashen leken asirin hukumar. Read more: https://hausa.legit.ng/1260088-yaro-ya-dabawa-mahaifinsa-wuka-har-lahira-a-jihar-kano.html

No comments:

Join our WhatsApp group

Join our WhatsApp group
Latsa nan domin shiga group din mu na whatsapp
Powered by Blogger.