YAN SANDA SUN CAFKE WANI MUTUM DA TSAUTSAYI YASA YA MARI MATARSA TA FADI TA MUTU

YAN SANDA SUN CAFKE WANI MUTUM DA TSAUTSAYI YASA YA MARI MATARSA TA FADI TA MUTU




Rundunar ‘yan sandan Legas ta kame wani mutum da
tsautsayi ya same shi bayan ya mari matarsa, ta fadi ta mutu
nan take.


Mai magana da yawun rundunar’yan sandan jihar Ogun, DSP
Abimbola Oyeyemi, ya shaida wa Aminiya cewa a ranar
Larabar da ta gaba ta ne mai Unguwar Atan da ke yankin
Sango Ota a jihar Ogun Rafiu Gbadomasi ne ya ankarar da
‘yan sanda suka kame mutumin mai suna Kingsley Madukwe
mai shekaru 40, dan asalin jihar Anambra da ke sana’ar acaba,
ya ce an samu karamar rashin jituwa ne tsakanin Kingsley da
matarsa Glory Madukwe mai shekaru 40.


Glory, ta haifa masa ‘ya’ya 8, ya ce matar na da karamin yaro
dan shekara daya, “A daren da lamarin ya faru, taron ya yi ta
tsala kuka abin da ya sanya Kingsley farkawa daga bacci ya
umarci matarsa da ta shayar da yaron nono, ita ko ta ce sam
baza ta iya shayar da shi ba domin ta gaji, nan ta tashi ta bar
masa yaron ta shiga turaka a daidai lokacin da yaron ke ci
gaba da tsala kuka lamarin da ya fusata shi ya wanke ta da
mari nan take ta fadi ta mutu.” In ji shi.



DSP Abimbola Oyeyemi, ya ce an kai gawar matar dakin ajiyar
gawa ta babban asibitin yankin domin zurfafa bincike, yayin da
aka tasa keyar Kingsley zuwa sashen binciken manyan laifuka
na rundunar ‘yan sandan jihar inda ake ci gaba da bincikarsa
kafin a gurfanar da shi a gaban kotu.

No comments:

Join our WhatsApp group

Join our WhatsApp group
Latsa nan domin shiga group din mu na whatsapp
Powered by Blogger.