WATA SABUWA: GWAMNAN JIHAR KASTINA AMINU BELLO MASARI ZAI SHIGA DAJI SUYI SULHU DA YAN BINDIGA




Gwamnatin jihar Katsina ta ce za ta tattauna da mutanen da
ake zargi da kai hare-hare da satar mutane domin karbar kudin fansa
don kawo karshen matsalar tsaro da take addabar jihar a kwana nan.


Daraktan yada labaran gwamnan jihar katsina, Audu Labaran, ya shaida
wa kafar yada labarai ta BBC cewa a wannan karon gwamna Aminu Bello Masari zai
shiga daji domin tattaunawa da 'yan bindiger.
Gwamnatin ta dauki wannan mataki ne yayin wani taron masu
ruwa da tsaki kan harkar tsaro da aka yi a fadar gwamnatin ta
Katsina.



Wannan dai na zuwa ne 'yan kwanaki kadan bayan wasu
mahara sun akfkawa garin Wurma a karamar hukumar Kurfi,
inda aka sace mata da dama.


Wadanda suka halarci wajen sun hada da gwamna da mataimakinsa
da sakataren gwamnati da Sarkin Katsina da shugabannin
hukumomin tsaro da shugabannin kungiyoyin Fulani da kuma
wasu masu kai hare-haren da suka ce sun tuba.


A cikin hirar, daraktan ya bayyana cewa a lokacin taron da aka
yi na Katsina da gwamnonin Arewa maso gabashin Najeriya an
amince cewa "kowacce jiha ya kamata ta kawo kudi ina jin
miliyan 100, a hada kudin nan, wato a hada karfi da karfe a
yaki wannan abin tun kafin ya zama wani abu daban" a
cewarsa.


Ya ce "to a bayan hakan ne gwamnonin suka yi shawarar ba
shi Ciyaman na din-din-din. Amma tun bayan taron babu wani
wanda ya kara waiwayar abin da aka yi ban da shi gwamna
Masarin".


A yan kwanakin nan dai hare-haren 'yan bindiga da satar mutane don kudin fansa na ci
gaba da karuwa a jihohin Zamfara da Katsina da Kaduna duk
da yunkurin jami'an tsaro na kawo karshen matsalar da ta
addabi yankin arewa maso yammacin kasar.
Mutane da dama ne dai suka rasa rayukansu, yayin da yara da
dama suka kasance marayu sakamakon kashe-kashen da ke
faruwa a jihohin.


Kananan hukumomin da matsalar ta tsafa a jihar Katsina sun
hada da Jibia da Batsari da Danmusa da Safana da Kankara da
Sabuwa da Faskari da kuma Dandume.

No comments:

Join our WhatsApp group

Join our WhatsApp group
Latsa nan domin shiga group din mu na whatsapp
Powered by Blogger.