DALILIN DA YASA MATAN HAUSAWA BASA IYA FURTA SOYAYYAR SU GA WANDA SUKE SO KO DA KUWA SUNA CUTUWA


Ma fi yawan mata na kasancewa cikin kunci da tunani mai
tsanani game da abin da suke so sai dai kuma wani sa’in kuncin
yana samuwa ne ta hanyar kuntatawa zuciyarsu musamman
wajen rashin yin dace ga abin da suke so din.



Wasu matan sukan cusa wa zuciyoyinsu soyayyar wani namijin
daban wanda bai ma san suna yi ba wanda Hausawa suke
kiransa da "SON MASO WANI-KOSHIN WAHALA" haka batun yake ba shakka domin kuwa bai san ma tana yi ba balle ya kula
ita kadai ta barwa zuciyarta sai kwana da take tana kwana da
shi ta wuni cikin tunaninsa....


Duk da dai ita soyayya Allah ke sakawa bawa cikin zuciyarsa ba
tare da yasan so din zai shiga ba, kai koda ace ya shiga ma
wasu sukan yi kokarin kawar da son dan gudun bacin rana ko
kuma abinda ka je ya zo wajen shi wanda suke so din ko dan
gudun wulakanci.



Kamar yanda su ma maza suke shiga halin ha’ula’i yayin da suke son
mace ba tare da ta san suna yi ba, ko kuma su furta mata taki
amincewa haka wasu matan ma suke tsintar kansu a ciki
wajen ingizawa zuciyarsu son wanda be san ma suna yi ba.


Sai dai akan samu akasi yayin da mace ta zamo cikin wannan
yana yi ta kasa fayyacewa wanda take so din soyayyar sa a
gareta dan gudun kar ya dauke ta bata san me take ba ko
kuma ajinta ya zube matsayinta na ‘ya mace, karshe kuma ta
barwa zuciyarta har ta cutu.


Wata kuma tana iya sanarwa da shi wanda take so sakon
zuciyarta ta ko wacce irin hanya ce sai kuma shi namijin ya
nuna ba ya sonta har ma ya samu hanyar da zai runka
wulakantata don kawai ta furta masa tana sonsa.


Baya laakarin idan shi ne ya kasance hakan ya zai zama a
gareta? Sai dai ya runka tunkawo yana fakakar wance ce take
sonsa shi ba ya sonta ya shiga wulakantata ta kowacce hanya
wanda inda shi ta yiwa hakan sai kowa ya ji labari a gari
wance na wulakanta wane ba ta kyauta ba.

Zaka iya karan


Yin nazari da tunani yayin furtawa wanda yake sonka kalma
me dadin sauraro koda kuwa kai ba ka sonsa na daya daga
cikin abin da zai kankaro maka/miki daraja a idon masoyi ko
masoyayar yi kokari ka farantawa wadda take sonka koda
kuwa kai baka sonta wajen tausar zuciyarta ta kyawawan
kalamai ba kalaman da zai bakanta mata zuciya ba.



Kar dai ku manta masoya duk abin da Allah ya tsara babu
tsumi babu kuma dabara sai ya faru kuma Hausawa suka ce
“MATAR MUTUM-KABARINSA” babu me auren matar wani
face Allah ya kadarta daman can matar ka ce haka in macen
ce ita ma wanda Allah ya kaddara ya zamo miji a gareta babu
yadda za ta zata shi za ta aura.



A rage wulakanta masoyi ko masoyiya koda kuwa ta furta
maka da bakinta, ko kuma tayi aike ga abokinka ko aminiyarta
domin a sanar maka da son da take maka tsananin so ke
kawo hakan don wata zuciyar na iya jurewa wata kuma
zuciyar bata iya jurewa har sai ta furta za ta iya samun
salama.



Soyayya na iya jefa masoyi ko masoyiya halin da sam! Ba a
iya tunanin fada wa haka ma wata kunyar takan iya raguwa
yayin da zuciya ta harbu ga wanda take so tsananin soyayyar
sai ta janye kunyar ta matsar gefe guda a sanarwa da juna.



Kalamai masu dadi na iya sawa koda namijin ba shida burin
auren macen daga baya in Allah ya kadarta matarsa ce sai yaji
soyayyarta ta fara ratsa cikin zuciyarsa a lokacin ne zai je ba
tare da jin wata kunya ba tunda daman ba wulakanta ta yayi ba
sabanin inda wulakanta yayi daga baya ya dawo ya ji
soyayyarta a zuciya ba zai iya komawa ya tunkareta ba sai dai
ya tura waninsa walau aboki ko kuma kawarta dan shawo
masa kanta.



Ku ci gaba da kasancewa da wannan shafi na SOYAYYA.COM.NG dan jin abubuwan da suka shafi soyayya har ma ga
masoya ma’aurata da kuma magance matsalolin soyayyar
daga gareku ta hanyar turo da sakonninku dan sauran masoya
su farga su gane wanda suka manta a tuna musu.

No comments:

Join our WhatsApp group

Join our WhatsApp group
Latsa nan domin shiga group din mu na whatsapp
Powered by Blogger.