CBN BAMU DAINA KARBAR YAGAGGUN KUDI BA SANARAWAR GAGGAWA DAGA TUSHE! BANKUNA BASU DAINA ANSAR YAGAGGUN KUDI BA.


SANARAWAR GAGGAWA DAGA TUSHE! BANKUNA BASU DAINA ANSAR YAGAGGUN KUDI BA....

Kamar Yanda jita jita tayi tasiri akan daina karbar yagaggun kudade kokuma wanda akayiwa liki, wannan Al-amarin ba gaskiya bane.

GA YANDA BATUN YAKE:-

Babban bankin Nigeria CENTRAL BANK OF NIGERIA ya kirkiro wani tsari na tsabtace kudaden kasarnan wato (CLEAN NOTES POLICY).

Wannan Sanarwa a tsakanin babban Bankin Kasa ne CBN da Sauran Bankina, a baya Idan Bankunan sunkai Kudi Ya gaggu a CBN akwai wasu kudade da aké karba daga hannunsu, Domin tsarkake kudaden masu dauda ko wadanda suka sha wuya shine Babban bankin yaba sauran Bankuna sanarwar cewa bazai karbi ko kobon suba a wannan tsakanin da aka bada sanarwa.

Idan sun kawo kudin CBN zasu karba batareda chajinsu ko sisi ba, dan haka wannan Sanarwa tsakanin CBN ne da sauran Bankuna.

Amma bankin bai hana yan kasuwa ko masu kananan sana'o i karbar yagaggun kudade ko masu liki ba kamar yanda jita jita tayi nisa cewar 30/8/2019 za'a daina karbar kudin.

Illa iyakadai mutane su guji ajiye kudaden dasuka yage agurinsu sabanin zuwa a canza musu ko kuma kaisu gurinda za'a kaisu bankin don canzawa.

A karshe muna kirada kananun yan kasuwarmu harma da manya, Dasu fahimci yanda abin yake su cigaba da karbar kudaden daga Customer har zuwa ranakun da'aka diba domin su zasu iya kaisu bankuna kuma a karba, sabanin malam talaka wanda baima san wata hulda ta banki ba.

Yakamata asanarda mutane don Allah kada a cutarda su babu gaira babu dalili, akwai wasu na zagayawa suna sayen yagaggun kudin wannan zalunchi ne babu wanda yasanyasu

Duk wanda yakeda yagaggun kudi yakai bankinshi zasu karba, Allah yasa mudache Amin

No comments:

Join our WhatsApp group

Join our WhatsApp group
Latsa nan domin shiga group din mu na whatsapp
Powered by Blogger.