ALAMOMI 20 DA ZAKA GANE KA KAMU DA SON MUTUM

ALAMOMI 20 DA ZAKA GANE KA KAMU DA SON MUTUM









Faɗawa a soyayya, na ɗaya daga cikin yanayin dake sakama mutane ɗoki da zumuɗi, saƙawa, da kuma tsoro a zukatansu.

     Idan ka fara son mutum, yana da wuya ka tuna yanda ka rayu a baya ba tare dashi ba, tabbas kana a raye kafin ka haÉ—u da wannan mutumen, anma baka fara rayuwa mai dadi ba, har sai da ku biyun kuka haÉ—u.


       Na tuna lokacin dana fara soyayya, naji tsoro sosai, nayi Æ™oÆ™arin kauce ma soyayya kafin na haÉ—u dashi, na tuna sanda yake burgeni, har zuwa sanda na fara sonshi, ya tashi daga wanda yake sakani murmushi, zuwa wanda yake bani farin ciki sosai a rayuwata, daga kyakkyawa, zuwa hadaÉ—É—en gayen dana taÉ“a sani a rayuwata

     Ka haÉ—u da wata tana burgeka kana tunanin koka fara sonta ne?  Mun zo muku da hanyoyi 20 da zasu tabbatar muku da tunaninku idan gaskia ne, insha Allah.


1- bugun zuciyarku na ƙaruwa sosai a duk lokacin da zaku haɗu

2- tunaninsu kawai na sakaka farin ciki

3- kana yawan duba wayarka, don kaga ko sun kiraka, ko kuma sun aje maka saƙo, ma'ana kowanne lokaci kana so su kiraka a waya


4- kana so kayi abinda zaka burgesu, suyi alfahari da ku


5- ko me kakeyi, zaka yi ta jin, dama suna tare dakai

6- koda wanne lokaci kana son kasancewa dasu, idan kana son mutum, baka taɓa gajia dashi.

7- mutum na farko daka farka da tunaninshi, kuma kayi tunaninshi ƙarshe kafin kayi barci, idan wani abin farin ciki ya sameka shi kake so ya fara sani, idan wani abun damuwa ya sameka, kana son goyon baya daga gareshi.

8. Ka fifita buƙatunsu fiye da naka, kafin na fara soyayya, ina da son kaina sosai, sanda na fara soyayya. Sai nake takura kaina indai zan mishi abinda zai faranta mishi. Haka soyayya take, buqatunka ba komai bane akan na masoyinka

9. Idan mutum yana burgeka, zakaji akwai abubuwa da yawa da zakayi dazai faranta mishi, anma fa ba komai ba, idan kuwa kana son mutum, zakayi koma menene domin ka faranta mishi.


10. Bazakaji kunyar faÉ—in yanda kake ji game da mutuminnan ba koma a ina ne, idan kana son mutum, kana son kowa ya sani.

11- duk wani mutum ajizi ne, masoyina shine mutumin da yafi burgeni, anma shima yana da ajizanci, anma a wurina na dabanne, halayene nashi da suke burgeni, so hanyoyi ne na karbar duk wani naƙasu na masoyinka.

12- idan kana son mutum, zaka ci gaba da hasaso rayuwar da zakuyi a tare, bazaka hasaso wani yanayi ba tare dashi a ciki ba, yanda zaku gina rayuwarku, idan kana son mutum duk wani tsari na rayuwarka zaka ringa yinta da shine.

13. Idan kana son mutum, babu wani yanayi dazai canja haka, idan ka fara tantama anya ina son wane? To tabbas ba sonshi kake ba, yana dai burgeka ne, kuma burgewa yana da iyaka, zai iyayin wani abin da bai burgeka ba.

14- idan ka fara son mutum, barci da cin abinci zasu maka wahala, saboda zumuÉ—in son kasancewa dasu.

15. Baka iya É—auke idanuwanka a duk sanda ka saukesu a kansu

16. Kana son haÉ—uwa da en uwansu da Abokansu

17- idan kana son mutum bazaka iya fushi da shi ba, saboda bazaka jure rashinshi ba koda na qanqanin lokaci

18. Idan kana son mutum, koda wanne lokaci zaka kasance cikin son bada labarinsa, duk inda ka zauna baka da wata magana sai tashi, kuma zaka kasance cikin farin ciki a duk sanda ake maka firarshi.

19. Idan kana son mutum, zaka kasance cikin alfaharin samunsa a koda yaushe

20. Babban dalilin da zaka gane kana son wani, tunda ka fara karanta alamominnan, shi kaÉ—ai kake tunawa a ranka
Rubutun
Rabiatu sk msh
Baby mashi

No comments:

Join our WhatsApp group

Join our WhatsApp group
Latsa nan domin shiga group din mu na whatsapp
Powered by Blogger.