MACE SAI DA GYARA, GYARAN AMARYA GYARAN FATA






▽・MACE SAI DA GYARAN JIKI・▽ □

GYARAN AMARYA ( 1 ) □
 ▾ dilka. ▾ lemon tsami. ▾ nescafe. Ki samu dilkar ki sai ki zuba masa nescafe ki matsa masa lemon tsami sai ki zuba masa ruwan zafi a Kai ki rufe shi. Zaki ga tadan kumbura zuwa anjima sai ki dinga Diba kina shafawa a jikinki. Zaki barshi zuwa wani lokaci har ya bushe a jikinki Daga nan sai ki dinga kankare shi Daga jikinki zaki dinga ganin dattin yana fita Daga jikinki zaki kuma ga fatar jikin ki tayi santsi Dan haka amarya sai a yiwa ango gyaran na musamman.


■ GYARAN AMARYA ( 2 ) ■
 ▾ kurku. ▿ du'aul Janna. ▾ humra. ▿ madale. A hada su waje daya a saka Dan ruwa kadan a kwaba a dinga shafawa a jikin fata zaki yi kyau sosai kuma kamshi zai Kama jikinki.


 □ GYARAN AMARYA ( 3 ) □
 ⇢man zaitun. ⇢ nono kindirmo. ⇢ kwal. sai ki hada su waje daya ki cakuda Daga nan sai ki dauka ki shafa a kan fuskarki Daga nan sai ki samu ruwan dumi kina tirarra fuskarki.


✿ GYARAN AMARYA ( 4 ) ✿
zaki iya samun cocumber ki shafa a kan fuskarki.


♜ GIDAN GYARAN AMARYA ( 5 ) ♜
✯ lalle. ✯ madara turare kafi-kafi. ✯ da'aul Janna. ✯ madara turare sultan. A hada su a kwaba su ko kuma a jika su tare da lalle ko kuma a dafa sai a tace ruwan lalle sai amarya ta dinga wanka dashi. Kuma zai Kama jikinta yayi kyau sosai. Bayan nan sai ki nemi turare wuta mai kyau mai kamshi ki dinga turara jikinki dashi.


□■ SABULUN GYARAN FATA ■□
 ➤ black soap. ⇢ septol. ⇢ Ghana soap. ⇢ sabulu salo. ⇢ dudu soap. ⇢ kurkur. ⇢ dilka. ⇢ ganyen magarya. ⇢ lalle. ⇢ madara turare. ki hada su waje daya ki burga su sai ki saka su cikin bokiti karami kina wanka dashi zaki ga yadda jikinki zai dinga yin kyali da kamshi ga uwa uba taushi da zai yi. ▃▃▃▃▃▃▃▃▃▃▃▃▃▃▃▃▃▃▃ ✯ MATAR DA MIJINTA KEDA KARANCIN MANIYYI ✯ sai ki rinka yi mishi miyar ayayo akai-akai yana sha. Ya yawaita shan tumaturi ya kuma rinka cin danyar kubewa miya, ya rinkayawan cin dankali,rogo, wake, zogale da tafarnuwa. ▃▃▃▃▃▃▃▃▃▃▃▃▃▃▃▃▃▃▃▃ ☜
(・FATAR JIKI ・)☞ kamar yadda kowa ya Sani ne fatar jiki itace wadda take lullube da jikin Dan Adam wato ta rufe kashi da fata. haka nan fatar jikin Dan Adam itace wacce take bayyana Duk wani Abu da zai fita Daga jikin Dan Adam na zafi ko sanyi, warin ko kashi. haka kuma ita kanta fatar jikin Dan Adam ta kasu ( 3 ) ● Akwai fata mai kuraje ( only skin ) ● akwai fata mai bushewa ( dry skin ) ☻ akwai fata mai fitar da warin kashi.


✿ YADDA ZAKI GYARA FAYAR JIKINKI ✿
gyaran fatar jiki ya kasu daban-daban kamar haka.
◇・FATAR JIKI MAI TAURI ・
◇ ⇨ shinkafa ( danya ) ⇨ ganyen darbejiya ⇨ rose water ⇨ kwan salwa Zaki barza shinkafa tafin hannu guda ki zuba a cikin yar'roba sai ki kwankwatsa ganyen darbejiya ki zuba sannan ki zuba rose water a ciki ki rufe ki saka a cikin firji, washe gari da safe sai ki fasa kwan salwa ki shafe jikinki da shi ki barshi har tsawon minti 30 sannan Kiyi wanka da ruwan dumi da sabulu mai kamshi, bayan kin wanke jikinki sai ki dauko wannan hadi na danyar shinkafa ki rinka murje fatar jikinki kamar yanda ake yin dilka zuwa minti goma sai ki sake dauraye jikinki da ruwan dumi ki tsane jikinki da tawul mai kyau sannan ki shafe fatar jikinki da man shafawa ma musamman na gyaran fata tauri na kwan salwa wato ( fairys salwa ) Idan kina haka Zaki ga fatar ki komai taurinta tayi laushi, tayi kyau. Idan kina wanna hadi na ( salwa facial scrub ) Zaki ga ke da kanki kin canja. Maigida ma kanshi sai kin zama abar alfahari ▃▃▃▃▃▃▃▃▃▃▃▃▃▃▃▃▃▃▃ ・

FATAR JIKI MAI GAUTSI ・ ▼ zuma ( FARAR SAKA ) ▼ kwan salwa. ▼ ruwan dumi. Zaki sami Zuma farar saka tattacciya sai ki fasa kwan salwa a ciki ki juyashi sannan ki shafe jikinki da shi ya rage 5m ko 10m ki shiga wanka sannan ki shiga wanka Kiyi wanka da sabulu ( salwa fairys soap ) Bayan kin turara jikinki da ruwan dumi Wanda kika tafasa kika rufe jikinki, minti goma sai ki wanke jikinki da ruwa mai dumi Zaki ji fatar jikinki tana sheki da kuma haske na musamman, sannan idan ma tana tsagewa ne to Zaki ga ta daina ta zama tubus, ta rinka sheki, kada ki manta bayan kin fito shafe jikinki da man shafawa na ( salwa fairys soap )

No comments:

Join our WhatsApp group

Join our WhatsApp group
Latsa nan domin shiga group din mu na whatsapp
Powered by Blogger.