ZAFAFFAN KALAMAN SOYAYYA GOMA NA NUNA TSANANIN KISHINKI A KAN SAURAYINKI




KALAMAN DA ZAKI DINGA YI WA SAURAYINKI DOMIN NUNA SOYAYYAR KI DA KISHINKI A KANSHI, SHIRIN DUNIYAR MASOYA soyayya.com.ng


 Duk lokacin da wata ta ce tana sonka ko ta nuna alamun tana sonka. Na rokeka masoyi ka taya ni kishin kanka ta hanyar dauke ta da mari sannan kace kai nawa ne ni kadai nima kuma haka zanyi wa duk wani saurayi da yace yana sona domin ni taka ce kai kadai


 Jama'a suna ganin duhu ne a cikin idanunsu yayin da dare yayi kuma wuta ta dauke. Ni kuma ina ganin duhu ko da kuwa da tsakar rana ce idan naji ance wa wata budurwarka. Saboda kishin ka da nake. Please ka kasance nawa ni kadai


 Bazan raga wa duk wacce tayi yunkurin raba ni da kai ba ya annurin zuciyata domin raba ni da kai dai-dai yake da raba ni da farin ciki na. Me zai sa wata ta so ka bayan ni. Na tabbata tsautsayi ne zaisa wata tace tana sonka habibina

KARANTA KUMA: NAFISA ABDULLAHI TACE BUHARI BAYA KISHIN AREWA TA KUMA CHA-CHAKE SHI

 Muradina duk lokacin da ka hangi 'yan mata a kan hanya tun daga nesa ka rufe idonka domin karka kalle su. I duk lokacin da ka rufe idonka da zarar kayi tunanina ni kuma zan wanzu cikin idanuwanka.


Zan iya jure ciwoka da cututuka iri daban-daban amma banda cutar rashinka. Domin kuwa dan adam yana sanin farin ciki ko bakin ciki ne ta hanyar zuciya sai dai kuma ni a halin yanzu bani d zuciya domin ka sace ta tun haduwata da kai ta farko masoyi.


Karka so wata bayan ni idan hakan ta faru ba zan sake farin ciki a cikin rayuwata ba. Ana dai cewa mata suna da kishi amma har yanzu banga mai kishi ba domin ba wacce take kishin saurayinta ko mijinta kamar yanda nake kishinka farin cikina. Kasa a ranka daga lokacin da ka furta kalmar so ga wata macen da bani ba daga lokacin numfashina zai dauke zuciyata ta daina bugawa


 Ba abu mai sauki bane zuciyar da ta dandani ukubar azabar so da soyayya ta sake yunkurin komawa cikin soyayya. Sai dai kuma kai gashi cikin sauki ka mantar da zuciyata wahalar da tasha a soyayya saboda kwarewarka ina maka son da bana yi wa kaina

 Visit Youtube/c/mamakitv for more subscribe


Domin kallon na video sai ku danna kan hoton nan


No comments:

Join our WhatsApp group

Join our WhatsApp group
Latsa nan domin shiga group din mu na whatsapp
Powered by Blogger.