SANIN SIRRIN SO DA KAUNA

ME NENE HAKIKANIN MA'ANAR SO?


Zuciyar wata ga6ace dake tura jini zuwa sauran sassan jikin dan Adam Inji masan . Amma a gaskiya. Zuciya itace wacce take zakulo mana wanda muka samu daidaiton jin da shi, sai ta ci gaba da bugawa dominsa.

Wannan dalilin yasa, idan muka tsaya dab da wacce muke so. Bugun zuciyarmu na karuwa ta sauri da sauti.
So shine, farincikinka ya sarkafu da farincikin wata. Ma'ana kana farinciki ne kurum da farincikinta.


So shine. Dankon dake damke ruhi biyu wuri guda, sannan ta cusa shi, cikin gan-gan jiki guda. Kafin ka ankare, sai ka ga, ta zama kai. Ka zama ita.

So shine, duhun da ke rufe idanuwan masoyi, ya hanashi ganin laifin masoyiyarsa. Wannan ake kira makanta, amma a zahirin gaskiya UZIRI ne da YARDA.

Hakikanin ma'anar soyayya. Shine, kulawa da juna, ko da bayan kun samu mummunan sa6ani.

So. Wata yanayi ne da farinciki masoyiyarka yafi muhimmanci akan na ka.
So. Wata kyal-kyali ne da ke haska duniyarka ciki da waje.


Daga: Abu-Ash'raf.

No comments:

Join our WhatsApp group

Join our WhatsApp group
Latsa nan domin shiga group din mu na whatsapp
Powered by Blogger.