ABUN AL'AJABI LABARIN SOYAYYA MAI TABA ZUCIYA

ABUN AL'AJABI
LABARIN SOYAYYA

ABIN AL'AJAB
I!!!
{Labarin so}
Duk abunda kakeyi dakata, ka karanta
wanan sakon,,,,
domin ganin darasinsa
Wani yaro ne dan shekara bakwai yana
cikin tafiya sai
ya tsinci wani hoto na wata yar
karamar yarinya itama
bata wuce shekara bakwai ba....
Wasa-wasa sai yaron nan yakamu da
sonta duk da
yake bai san kowacece ba...
Kullum in zai kwanta barci da hoton
yake kwanciya,
idan ya gama kallon hoton sai ya daga
filonsa ya
boye... Wani lokacin kuwa yana cikin
kallon hoton barci
yake saceshi....
Abokanan shi har zolayarsa suke suna
ce masa me
hoton tsintuwa...
A takaice dai har yayi aure yana ta
ajiyar hoton nan..
Wata rana sai matarshi taga hoton sai
tace me gida a
ina kasami wannan hoton? Sai yace
tun ina dan
shekara bakwai na tsince shi, ina ta
ajiyarsa har zuwa
wannan lokacin....
Nan take sai kwalla ta zubo daga
idanuwanta tace
lallai Allah shine me iko to ai wannan
hoton nawane,
tun ina karama ya bace min....
Nan take suka rungume juna suna
kuka. Bayan sun
gama kukan dadi, Sai yayi sujjada ga
Allah yana mai
godiya gareshi daya hadashi da wadda
yake so tun
yana dan karami.



ABIN LURA ANAN........
1. Kasani cewa Allah shi kadaine me
iko, shi yake
hukunta abinda yaso.
2. Kaddara bazata taba gushewa ba,
abinda Allah ya
kaddara shi yake tabbata.
3. Matar mutum kabarinsa, matarka ko
a ina take sai
tazama matarka kome rintsi, ko ana
ha-maza ha-mata,
saboda haka kada ka taba fada da
wani akan budurwar
da kake so, ko kuma saurayin dakike
so. Dan rabo

baya wuce maishi.

Zaku iya turo labarai na kwarai ta duniyarso1@gmail.com

No comments:

Join our WhatsApp group

Join our WhatsApp group
Latsa nan domin shiga group din mu na whatsapp
Powered by Blogger.